Ƙaramar hukuma ta gargaɗi malamai su guji fashin zuwa aiki

Spread the love

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Shugaban ƙaramar hukumar Malam Madori da ke Jihar Jigawa ya yi barazanar ɗaukar matakin hukunta malaman makaranta da ba sa zuwa aiki kullum.

Shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Salisu Sani Garun-Gabas ya bayyana haka a wata hira da manema labarai bayan raba kuɗi dubu hamsin hamsin a matsayin tallafin karatu ga ɗalibai ashirin da biyar a yankin.

A cewarsa, wani bincike da aka gudanar bayan hawansa karagar ƙaramar hukumar mulkin Malam Madori ya nuna cewa malaman makarantu da dama ba kasafai suke zuwa aiki ba.

Ya ce hakan na daga cikin dalilan da yasa aka Sami taɓarɓarewar ilimi a yankin, wanda ke buƙatar kulawar gaggawa.

Alhaji Salisu Sani Garun-Gabas ya yi nuni da cewa, “Ilimi muhimmin abu ne a kowane fanni na rayuwar ɗan Adam, don haka ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wani malamin da ba ya zuwa makaranta”.

Ya yi nuni da cewa, akwai mutane da dama waɗanda suka kammala karatu kuma ba su sami aiki ba, saboda haka za a iya ɗaukar su aiki domin maye gurbin waɗanda ba sa son zuwa aiki.

Shugaban ƙaramar hukumar ya kuma shawarci matasan yankin da su sadaukar da kansu wajen samun ilimi mai inganci, domin cigaban rayuwarsu da ƙasa baki ɗaya.

Ya ƙara da cewa, ƙaramar hukumar a ƙarƙashin jagorancinsa za ta cigaba da bayar da tallafi ga ilimi ga ɗalaibai, domin ganin an ƙarawa matasan da suke da niyyar yin karatun ƙwarin gwiwa wajen neman ilimi.

By ukarofi