Da Ɗumi-Ɗumi: Obasa ya koma Kakakin Majalisar Dokokin Legas bayan Meranda ta yi murabus

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

An sake zaɓar ɗan majalisa da ke wakiltar mazaɓar Agege ta 1, Mudashiru Obasa a matsayin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Legas.

A ranar Litinin ne aka sake zaɓar sa, biyo bayan murabus da Mojisola Meranda ta yi daga muƙamin.

An zaɓi Obasa ne bayan goyon baya da ya samu daga tsohon jagoran mafiya rinjaye na majalisar, Noheem Adams da ke wakiltar Eti-Osa ta 1.

Hallau a ranar ce Miranda ta sauka daga muƙamin, inda kuma ƴan majalisar suka zaɓe ta a matsayin mataimakiyar kakakin majalisar.

Miranda ta ce, ta yi hakan ne don kare martabar majalisar, tana mai cewa ba miƙa wuya ta yi ba.

By Babaji