Ƙungiyar Moppan reshen Jihar Yobe ta kai ziyara fadar Mai Martaba Sarkin Machina, Dr. Alhaji Bashir Albishir Bukar (OON), yayin da ƙungiyar ta nemi goyan bayan masarautu da su yi wa masana’antar Kannywood kyakkyawan fahimta da kuma fatan alheiri.
Sarkin ya yi farin cikin jin hakan kuma ya bada shawara da a dinga tsayawa akan al’adarmu, kuma ya ƙara da jaddada goyan bayansa ga Kannywood.

