ILO ta horar da masu ruwa da tsaki kan tsaron sana’o’i da kawar da bautar da ƙananan yara aikin haƙar ma’adinai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A kokarinsu na ganin an kawo ƙarshen bautar da ƙananan yara da ake yi a Nijeriya, Ƙungiyar da ke kula da Manya da Ƙananan wuraren hakar Ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba (ILO), ta gudanar da taro daga ranar 18 zuwa 27 ga watan Fabrairu na 2025 a jihohin Neja da Osun.

Manufar taron dai ita ce
ƙarfafa gwiwar masu ruwa da tsaki tare da wakilai daga cikin gwamnati, ma’aikata daga ƙungiyoyi tare da shugabannin yankunan domin kawo ƙarshen aikin bautar da ƙananan yara da ake yi a wuraren.

Hakazalika, an bai wa mambobin kwamitin da ke sanya ido kan ayyukan bautar da yara na jihohin da kayan aiki da za su taimaka wajen sanya ido, da kuma kai rahoton duk wani aiki na bautar da yara ƙanana.

Daraktan ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa, Dr. Vanessa Phala, wadda ta samu wakilcin mai kula da ayyuka na ƙungiyar ACCEL Africa, Mrs.Celine Oni, ta bayyana cewa an yi taron bitar ne domin ƙarfafa wa masu-ruwa-da-tsaki tare da cibiyoyin da ke yaƙi da bautar da yara ƙanana, sannan ta jaddada cewa za a aiwatar da dokoki da tsare-tsare da za su taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar.

Ƙudirin farko na shirin ACCEL Africa shine, aiki tare da hukumomi irinsu Ma’aikatar kwadago da bunƙasa ayyukan yi ta ƙasa, da Ma’aikatar Noma, Ma’aikatar da ke kula da Ma’adinai da dai sauransu.

Na biyu shi ne, ɗaukar mataki kan musabbabin bautar da yaran ke yi ta hanyar samar da mafita bayan samun damar gudanar da bincike a yankunan da ake haķar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, sannan za a mai da hankali sosai kan muhimman fannonin samar da kariya, kudade, kiwon lafiya da samar da aikin yi ga matasa.

Daraktar ta jaddada cewa za a magance dalilin haddasa wannan aiki na bautar da yara, wanda ta ce talauci da rashin samun kariya ne kan gaba wajen haifar da wannan matsala.

Kwantirola ta ma’aikatar ƙwadago da bunƙasa ayyukan yi ta ƙasa reshen Jihar Neja, Hauwa Zakariyya, ta ce, “samar da tsaro da kuma kiwon lafiya hakki ne da ya rataya a wuyan kowa, sannan ba za a samu wata ci gaba ba ma damar babu tsaro, don duk wasu munanan al’amura za su iya faru wa a wuraren aiki idan har ba a dauki matakin kare kai a lokacin da mu ke tsaka da aiki.”

“Don haka ne ma mu ke daukar wannan kungiya ta ACCEL Africa da muhimmanci, wacce ta mai da hankali kan wuraren haķar ma’adanai manya da ma kanana, domin kare kai daga mummunan al’amari makamancin abin da ya faru a yankin Kuchiko, inda aka rasa rayuka da dama da su ka hada da kananan yara. Mun yi imanin cewar wannan tsari zai ilimantar da masu hakar ma’adanai yadda za su kare kansu anan gaba.”

A nasa ɓangaren, Kwantirola na ma’aikatar ƙwadago reshen Jihar Osun, Mr.Solomon Ayinde Alabi, ya bayyana matuƙar farin cikinsa kan wannan aiki a jihar, duk da cewa ba ta gajiyar shirin ba na farko, amma dai shirin zai amfane su kamar yadda ya amfani sauran jihohi irin su Ondo da Neja wanda aikin ya kawo sauyi mai kyau.

Ya ce, “ɗaya daga cikin amfanin shirin shi ne, rahoton da ke fitowa daga yankin Ibala. Muna murna da cewa, rahoto ya tabbatar da cewa ficewar yara daga makarantu ya ragu sosai. Wannan babban labari ne gare mu a irin wadannan yankuna.”

“Ina kuma yin kira gare mu a matsayinmu na iyaye, masu kulawa, da al’umma da mu yi amfani da wannan dama da kyau wajen kara azama wajen yaki da ta’addanci, bautar da yara a yankunan mu”, inji shi.

Waɗanda suka halarci taron sun ziyarci wuraren haƙar ma’adanai a jihohi mabanbata don duba yadda ake gudanar da ayyukan, inda suka yi arba da kayan aikin kamar na’u’rori, tare da gano hadarin da ke tattare da wannan aiki.

A cikin tattaunawa da Lawali Yusuf mai shekaru 13 cikin yara masu haƙar ma’adanai a Korokwa da ke Minna na jihar Neja ya ce, “ina wannan aiki ne saboda iyaye na ba su da ƙarfin ɗaukar nauyin karatuna, don haka na yanke shawarar yin wannan aikin saboda na tara kuɗi na fara zuwa makaranta kamar sauran abokaina. Na san aikin hakar ma’adanai yana da matukar hadari, amma bani da wata mafita bayan aikin.”

A yankin Idoka dake Osun, wani ɗan shekara 11 me suna Ibrahim da ke hakar ma’adanai ya ce, “burina shi ne zama mai hakar ma’adanai idan na girma, don haka ne ma na zo nan a matsayin yaron gida. Ina so na koyi yadda ake gaƙo zinari duk da cewa sau da dama ana korata daga wurin, sai dai ina dawowa saboda muradina kenan zama mai haķar ma’adanai.”

Wannan taro dai ana tunanin cewar zai kawo sauyi wajen yyaki da bautar da yara musamman a ɓangaren haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.

By Babaji