Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ayyukan samar da ruwan shan sun haɗa da gina da gyara madatsun ruwa a garin Ɗanja, yashe a ƙananan hukumomin Ɗanja da Kusada.
Mataimakin gwamnan jihar malam Farouk Lawal Joɓe ya sanar da haka da ya ke hira da manema labarai kan nasarorin da gwamnatin jihar ta samu kan harkan noma da samar da ruwan sha.
Ya ce Naira biliyan 5.8 gwamnatin jihar ta kashe wajan gina da gyara wannan madatsun ruwa da kuma inganta ɗakin gwaje gwajen ruwa da ke Ɓatagarawa da garin Musawa.
Haka kuma gwamnati ta samar da wani famfon tura ruwa mai karfin kilowatt 80 da bawuloli 121 a madatsar ruwa ta Ajiwa tare da inganta wutan lantarki a madatsar ruwan.
“Gwamnati kuma ta Kashe Naira biliyan 14.4 wajen samar da ruwa a sassa daban daban a jihar ƙarƙashin shirin SUWASH”inji joɓe.
Ayyukan kuwa a cewar sa sun haɗa da samar da ruwan sha a unguwanni Tudun Matawalle, Rukunin gidajen Sardaunan,Fatima Shema,Ambasada, Asibitin kwararru na Katsina da garin Ɓatagarawa.
Haka kuma mataimakin gwamnan ya sanar da kammala aikin ruwan sha a unguwannin rukunin gidajen Dutsen Safe,Rahamawa,Abatuwa da Sabuwar Unguwa.
Sauran unguwannin da aka kammala aikin ruwan akwai Tudun ‘yan lihidda,rukunin gidajen Barhin,kofar Durbi,Maƙera, unguwar Saulawa, Tudun Wada, Rafin daɗi da sauran su a cewar Joɓe.
An gudanar da irin wannan aiki a unguwanni da ke ƙananan hukumomin Malumfashi da Funtua ya ce.
Gwamnatin Katsina ta kuma kammala gina tankunan tara ruwa guda biyu masu cin adadin lita 450,000 a unguwar Tayoyi a garin Katsina da cibiyar tara ruwa a garin Tsanani da ke ƙaramar hukumar Ɓatagarawa, mataimakin gwamnan ya bayyana haka.
Ya ce akwai aikace-aikace da dama da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta aiwatar kan abinda ya shafi samar da ruwan sha a faɗin jihar da ba a faɗa ba
Farouk Joɓe ya bada tabbacin cewa gwamnatin Dikko Raɗɗa,za ta cigaba da yin tsare-tsare da aiwatar da shirye shiryen da za su kawo ci gaba mai ɗorewa a jihar.
