
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wata ƙungiyar al’ummar Fulani da ke ƙarƙashin Haɗakar Ƙungiyoyin Fulani, ta gargaɗi gwamnatin Jihar Filato akan sabon umarnin harbi ga dukkan wanda aka samu yana lalata gonaki a faɗin jihar.
Hakan na zuwa ne bayan kalaman Gwamna Caleb Mutfwang a lokacin wata ziyarar ta’aziyya a Ƙaramar Hukumar Barikin Ladi, sakamakon wasu sababbin hare-hare da rikici da aka yi a kwanan nan.
A cewar rahotanni, Gwamna Mutfwang ya umarci hukumomin tsaro da su ɗauki matakin da ya dace akan wanda aka samu da hannu a lalata gonaki yayin da rashin tsaro ke ƙara ƙamari, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 50 a cikin tsawon wata guda da ya gabata.
Da take tsokaci akan umarnin, ƙungiyar Fulanin ta bayyana shi a matsayin haɗari, inda ta yi gargaɗin cewa hakan ka iya faɗaɗa fargaba a jihar matuƙar ba a sake nazari a kai ba.
Don haka ne ta yi kira ga gwamnatin da ta ɗauki matakin tattaunawa, adalci da hanyoyin warware rikici cikin salama akan waccar matsayar da ta ɗora al’umma a kai.
Haka kuma, ƙungiyar ta roƙi hukumomin tsaro da su cigaba da nuna ƙwarewa wajen sauke nauyin ayyukansu da kauce wa ɗaukar matakan da ka iya shafar mutanen da ba su ji ba ba su gani ba musamman a yankunan da ke fama da rikice-rikice.
Wannan ci-gaba na zuwa ne a daidai lokacin da Jihar Filato ke cigaba da fuskantar matsalolin rikicin fili, ayyukan gonaki da na ƙabilanci a sassa da dama na ƙananan hukumominta.
Mazauna da masu ruwa da tsaki na cigaba da kira akan ɗaukar matakan tsaro masu ƙarfi tare da yunƙurin sasanci tsakanin ɓangarorin da ke rikici a junansu da nufin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a faɗin jihar.
