Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
‘Yan bindiga sun kashe mutane tara ciki har da ɗan banga (Forest Guard) da mace mai juna biyu a ƙaramar hukumar Bakori na jihar Katsina.
Ɗan majalisar dokoki mai wakiltar ƙaramar hukumar Bakori Hon Abdulraham Ahmad Kandarawa ya sanar da haka a hira da manema labarai a Katsina.
Ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun shiga ƙauyen Gidan Wawu da ke mazaɓar Guga inda suka kashe mutanen tare da raunata mutane biyar da yanzu haka suna asbiti suna amsar magani.
Kandarawa ya ce tuni aka yiwa waɗanda suka rasu sutura.
Ya Kuma bayyana cewa bincike da suka yi ya nuna yan bindigan da suka aikata wannan mummunar ta’asa da waɗanda akai sasancin da su ba ne domin suna shigowa gari ana magana da su.
A cewar ɗan majalisar bincike da suka yi ya nuna cewa yan bindigan da suka aikata wannan barna sun fito daga jihar zamfara ne domin “ko da suka taso kafin su iso ana ta buga mana waya cewa sun tsallako amma bamu san inda suka nufa ba.
