Daga ABUBAKAR A BOLARI GOMBE
Sanata Muhammad Danjuma Goje ya yi watsi da sakamakon zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC na kujerar Sanatan Gombe ta Tsakiya, inda ya bayyana sakamakon da ake yaɗawa a matsayin na bogi.
Wani sakamako da jami’in tattara sakamako, Dakta Habu Ɗahiru, ya bayyana ya nuna cewa DCP Mohammed Ahmed ne ya lashe zaɓen tare da zama ɗan takarar jam’iyyar a babban zaɓen shekarar 2027, bayan da ya samu ƙuri’u 42,785 yayin da Sanata Goje ya samu ƙuri’u 10,425.
Sanata Goje na wakiltar mazabar sanatan tun daga shekarar 2011.
Sai dai a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman, Ahmed Isa Kashere, ya fitar, Sanatan ya ce har yanzu ba a kammala tare da sanar da sakamakon zaɓen fidda gwanin kai tsaye da aka gudanar ranar Litinin a ƙananan hukumomin Akko da Yamaltu/Deba ba, waɗanda su ne ƙananan hukumomin da suka haɗa Gombe ta Tsakiya.
“Duk da cewa har yanzu ba a sanar da sakamakon hukuma ba, wasu kafafen yaɗa labarai da shafukan sada zumunta sun cika da sakamakon ƙarya da ake cewa wai shi ne sakamakon zaɓen,” in ji sanarwar.
Sanata Goje ya buƙaci al’ummar mazabar, magoya bayan jam’iyya da kuma jama’a gaba ɗaya da su kwantar da hankalinsu tare da yin watsi da “sakamakon bogi da ake yaɗawa.”
Sanarwar ta ƙara da cewa:
“A madadin Sanata Muhammad Danjuma Goje, ina sanar da al’ummar Gombe ta Tsakiya da ta ƙunshi ƙananan hukumomin Akko da Yamaltu/Deba da su yi watsi da sakamakon bogi da maƙiyan jam’iyyarmu ta APC ke yaɗawa a matsayin sakamakon zaɓen fidda gwani na Sanatan Gombe ta Tsakiya.
“Domin kauce wa shakku, har yanzu ba a sanar da sakamakon hukuma na zaɓen ba. Bisa ƙa’idojin da hedikwatar jam’iyyar APC ta ƙasa ta fitar, za a sanar da sahihin sakamakon ne a Abuja.”
Ya kuma buƙaci dukkan ‘yan jam’iyya, magoya baya da sauran jama’a da su kasance masu haƙuri su jira sanarwar hukuma ta sakamakon zaɓen.
“A matsayinsa na ɗan majalisa mai daraja kuma dattijo a siyasa, Sanata Goje na ci gaba da bin doka da oda tare da mutunta ƙa’idoji da dokokin jam’iyyar,” in ji sanarwar.
