Ƙungiyar GOBA 94 ta ziyarci kwamandan rundunar sojojin sama na Kano

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Shugaban rundunar 455 Base Services Group na sojojin sama na Kano, Group Captain Mustapha Suleiman, ya yaba wa abokan makarantar sa na Gwale Old Boys Association, ajin 94 (GOBA 94), kan ziyarar girmamawa da suka kai masa a hedkwatar rundunar.

A jawabin sa, Group Captain Suleiman ya bayyana ziyarar a matsayin babban girmamawa gare shi da dukkan ma’aikatan rundunar. Ya kuma gode wa shugaban GOBA 94, Alhaji Bello Ɗan-Bappa, shugabanni, da dukkan mambobi kan tunanin alkhairi.

Ya ƙara tabbatar da kishin sa ga ƙungiyar tare da yi musu addu’ar lafiya, kariya, da jagoranci daga Allah.

Haka zalika, ya jaddada muhimmancin kasancewa cikin zumunta da abokan makaranta tare da nuna girmamawa ga tushen rayuwar mutum. Ya ce wannan ziyara ta ƙara haskaka alaƙar da ke tsakaninsu tun lokacin makaranta, wanda ke nuna irin zumunta da haɗin kai na musamman da suke da shi.

A jawabinsa, Shugaban GOBA 94, Alhaji Bello Ɗan-Bappa, ya bayyana ayyukan jin ƙai na ƙungiyar kamar rabon kayan sawa lokacin Sallah, bayar da tallafi wajen aure, taimakon magani, da kuma kula da iyalan marasa rai. Ya kuma sanar da zaɓukan kwanan nan da suka gudana, inda aka zabi Nura Garba a matsayin PRO na ƙasa. Ya yi kira ga kwamandan da ya ci gaba da taka rawa a cikin ƙungiyar don kara danƙon zumunci.

By ukarofi