Tsohon Ministan Abuja, Janar Jeremiah Useni ya rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A daren ranar Alhamis ne Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato ya tabbatar da rasuwar Laftanal Janar Jeremiah Tumbut Useni, mai shekaru 82 da haihuwa, bayan fama da wata jinya ta tsawon lokaci.

A wata sanarwa da Kakakin gwamnan, Gyang Bere ya fitar, Gwamna Mutfwang ya ce ba iya iyalan babban jami’in aka yi wa rashi ba, har da rundunar sojoji da ma ƙasa baki ɗaya.

Gwamnan ya kuma ce irin jagorancin marigayin na jajircewa wajen yi wa ƙasa hidima abin koyi ne acikin al’umma, ya na mai cewa mutuwarsa ta bar giɓi a harkokin tsaro da siyasar Nijeriya.

Ya ce za a cigaba da tuna irin namijin ƙoƙarinsa ga samar da zaman lafiya da tsaro a arewacin Nijeriya musamman a jihar Filato.

Kazalika, gwamnan ya bayyana irin gudummawar da Janar Useni ya bayar a harkar siyasa inda ya taɓa riƙe muƙamin mataimakin shugaban jam’iyyar ANPP da kuma lashe zaɓen kujera sanata a Filato ta Kudu ƙarƙashin jam’iyyar PDP, a shekarar 2015.

Har’ilayau, ya miƙa ta’aziyyarsa a madadin gwamnatin jihar ga iyalai da Shugaban ƙasa da rundunar sojoji da dukkan ƴan uwa da abokan arziƙi bisa babban rashin da aka samu, ya na mai fatan samun juriya a gare su.

By Babaji