Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
An gabatar da wannan horarwa na koyar da sana’o’i ga marayun ƙarƙashin ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah ta Jihar Katsina haɗin gwuiwa da Gidauniyar Sautus Sunnah Charity Foundation.
A jawabin sa wajen bikin shugaban ƙungiyar Izalatul bidi’a wa Ikamatul sunnah reshen jihar Katsina Sheikh Yakubu Musa Hassan Sauttus sunnah ya bayyana cewa Sanata Sadiq Yar’adua ya miƙa wannan cibiya ga kungiyar Izala ta jihar wanda ita kuma bisa wannan ne ƙungiyar ta yi haɗin gwiwa da Sautus-Sunnah Charity Foundation domin koyar da marayu matasa maza da mata sana’o’in hannu “domin a taimaki marayun da mu ke da su a wannan jiha ta Katsina ta hanyar koyar da su ilimin addini da na zamani tare da koyar da su sana’o’in hannu,”Inji Sheikh Yakubu Musa.
Muna cikin farin ciki na ganin mun haɗu a wannan farfajiyar domin yaye ɗalibai sama da 300 da aka koyar wanda mun fara ganin yadda ɗaliban su ka maida hankali tare da ɗaukar abinda aka koyar da su da muhimmanci,”Sauttus Sunnah ya ce.
Ya bada tabbacin Gidauniyar Sautus-Sunnah Charity Foundation za ta cigaba da gabatar da wannan horaswa inda za’a ɗauki ɗalibai karo na uku nan bada jimawa ba.
Sheikh Yakubu Musa ya yi addu’a ga Sanata sadiq Yar’adua muna rokon a dinga sanya Sanata Sadiq bisa samar da gidan marayu da yayi,ya kuma yi fatan al’ummar musulmi za su yi koyi da Sanatan.
Ɗaliban sun gabatar da abinda su ka koya a fanni daban daban .
Marayun sun sami horo akan kayan lantarki da na ruwan sha ,walda, kafinta,ɗinkin keke,da gyaran takalma.
Haka dalibai sun gabatar da karatun Al-Qur’ani Mai Girma a ɓangaren Islamiyya.
Taron ya gudana ne a farfajiyar makarantar da ke garin Kaita hanyar Yanhoho.
Wanda ya samu halartar; Babban Daraktan Gidauniyar Sautus Sunnah Charity Foundation Sheikh Saifiddeen Yakubu Musa, Alh. Usman Nadada, Sheikh Dr. Abdulkadir Saleh Kazaure, Sheikh Dr. Ismail Kumo, Sheikh Abubakar Abdussalam Baban Gwale, Sheikh Abdulbasir Isah Unguwar Maikawo, Wakilin Hakimin Kaita Galadiman Yandaki Alh. Bello Abubakar Yandaki, Wakilin Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Katsina, Wakilin Kwamandan NSCDC da sauran mayan malamai.
