Ƙungiyar KADDA ta gudanar da taron shekara

Spread the love

Daga WAKILINMU

Cikin ‘yan kwanakin nan ne kungiyar cigaban cikin garin Kaduna, Doka, Wato KADDA ta gudanar da taron ta na shekara-shekara, inda Shugaban kungiyar, Honorabul Sani Rabi’u Bako ya bayyana nasarorin da su ke samu da cewa wani al’amari ne daga Allah madaukakin Sarki.

Honarabul Bako ya bayyana haka ne a lokacin da ya tattauna da manema labarai, jim kadan bayan kammala taron kungiyar na bana, inda aka gabatar da muhimman jawabai da kuma bayar da satifiket da lambobin karramawa na shekarar 2023.

Sani Rabi’u Bako, ya ci gaba da cewa duk da wannan Kungiyar ba ta siyasa ko samun kudi ba ce, amma dai ta na gabatar da muhimman ayyuka a bangarorin ciyar da al’umma gaba.

A nan ya kawo misalin wasu abubuwan da su ke aiwatarwa, wadanda suka hada da taimaka wa Marayu, koya wa yara sana’o’i, koya wa matasa karatun dabarun yadda za su rubuta jarabawar NECO da WAEC da kuma JAMB da nufin samun manyan gobe masu ilimi da hazaka.

Ya ce kuma kungiyar na gabatar da aiki a kan samar da Zakka da raba wa mutanen da suka cancanci a ba su da suke a cikin jama’a.

“Ba kungiya ba ce ta cin riba ba, sai dai kawai ana yin ayyukan ne domin a taimaka wa jama’ar yankin mazabun Doka, Shaba, Gaji da Mazabar Liman duk a cikin yankin Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa.

“Muna kuma taimaka wa Mata masu bukatar taimako da marayu ta hanyar sana’o’i da sauran su, da masu fitar da zakka a raba wa al’umma da ba su da hali. Muna kuma bi domin tabbatar da cewa akwai zaman lafiya a wannan yankin.”

Da yake gabatar da qasida a wajen taron, Farfesa Kabiru Isah daga Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, dogon jawabi ya yi a kan muhimmancin ilimi da kuma irin yadda ake samun cigaba a wajen tafiyar da al’amuran duniya, musamman ta hanyar yin amfani da yanar Gizo.

Farfesa Kabiru ya yi kira ga daukacin al’umma da su hanzarta rungumar hanyoyin samun cigaba na zamani domin gudun kada a bar su a baya.

Shi kuma cikin tasa kasidar mai taken ‘gudunmawar matasa wajen cigaban al’umma’, Dokta Aliyu Adamu Isah bayyana matasa ya yi da cewa mutane ne masu matukar muhimmanci a cikin al’umma.

Ya ce, “Matasa za su iya bayar da gagarumar gudunmawa wajen cigaban kasa da al’umma bakidaya.

“Kuma ya dace matashi ya zama mai dogaro da kansa a kodayaushe, ya kuma riqa yin aiki da kula ta hanyar tabbatar da ‘yan uwantaka tsakaninsa da juna, matashi ya riqa danne zuciya a kodayaushe kafin gabatar da al’amura.

“Sai dai ya dace a rika karfafa wa matasa domin ba su kwarin gwiwa, domin matasa na saurin yin gangamin tara sauran matasa ‘yan uwansu a duk lokacin da wani abu ya faru.

“A rika sauraren matasa a na shigo da su a cikin gudanar da harkoki na yau da kullum ta yadda za a rika Koyar da su a kodayaushe.

“Saboda a mafi yawan lokuta idan matashi ya ga karatu ko makaranta ba za su ba shi abin da yake bukata ba, sai ya koma ya nemi wani abin daban da yake ganin zai ba shi abin da yake so, don haka sai an yi a hankali a kodayaushe.”

Jama’a da dama ne dai suka gabatar da jawabai a wurin wannan taro da ya tara dimbin mutane.

By Editor