Don amfanin ƙasa na ɗauki tsauraran matakai – Tinubu

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Shuagaban Kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa, tsauraran matakan da ya dauka tun bayan da ya karbi ragamar mulkin kasa, ya yi hakan ne domin ceto Nijeriya daga fadawa halin ha’ula’i.

Tinubu ya bayyana haka ne a jawabin sabuwar shekarar da ya yi wa ‘yan kasa da safiyar ranar Litinin, wanda aka yada kai tsaye a kafafen yada labarai.

A cewarsa, “Dukkan abin da na yi a ofis, duk wani mataki da na dauka, duk wata tafiya da na yi zuwa wajen kasa tun bayan da na shiga ofis ran 29 ga Mayun 2023, na yi hakan ne saboda amfanin kasarmu.

Ya kara da cewa, “Sama da wata bakwai da kafuwar gwamnatinmu, na dauki tsauraran matakai domin ceto kasarmu daga afkawa cikin halin ha’ula’i.

“Daya daga cikin matakan shi ne cire tallafin mai, nauyin da kasa ke dauka na gomman shekaru wanda a yanzu ba za ta iya ci gaba da dauka ba.

“Wani matakin har wa yau, shi ne gyara tsarin musayar kudaden waje wanda wasu masu kumbar susa ne kawai suke amfana.”

Shugaban Kasar ya ce babu shakka, waɗannan matakai guda biyun da aka dauka sun haifar da rashin jin dadi ga wasu ‘yan kasa da harkokin kasuwanci.

Tinubu ya yi amfani da wannan dama wajen taya ‘yan Nijeriya murnar shiga sabuwar shekarar 2024. Tare da kira a gare su da ci gaba da mara wa gwamnatinsa baya domin ba ta damar yi wa ‘yan kasa hidima yadda ya kamata.

By Editor