
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Ƙasa (NARD), ta dakatar da yajin aikin gama-gari da ta tsunduma a yau Talata.
Da yake ganawa da manema labarai a ranar, Shugaban NARD, Mohammed Usman Suleiman an cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa da majalisar zartarwar ƙungiyar, inda a nan aka umarci dukkan likitoci su koma aiki da misalin ƙarfe 8 na safiyar ranar Laraba.
Suleiman ya bayyana cewa, NARD ta samu tabbaci daga Gwamnatin Tarayya akan sauya matakin janye aiwatar da tsarin biyan alawus ga mambobin na PAT, wanda zai fara a watan Afrilun 2026.
Akan haka ne ƙungiyar ta bai wa gwamnatin wa’adin kwanaki 21, wanda matuƙar ba a cika alƙawarin ba, to lallai za ta tsunduma a yajin aiki.
NARD da gwamnatin sun cimma yarjejeniyar fara biyan ma’aikata alawus ɗin PAT bayan yajin aiki na tsawon lokaci a 2025
Yarjejeniyar ta ƙunshi ƙarin kuɗaɗen alawus na zuwa aiki, aikin dare, da kuma alawus ɗin tura likitoci zuwa karkara domin inganta walwalarsu, duk kuwa da cewa an yi tsammanin fara aiwatar da tsarin a farkon watan Janairu ko Fabarairu 2026.
A cewar ƙungiyar, wannan mataki ya rushe yardar da ta yi wa gwamnatin da kuma karya alƙawarin da aka yi a baya tare da buƙatar gaggauta aiwatar da matakin da biyan su dukkan bashin da suke bi.
