
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wasu ‘yan bindiga sun yi wa wani ɗalibin Jami’ar Ilimi ta Tarayya da ke Pankshin kwanton-ɓauna tare da halaka shi a ƙauyen Dum da ke Gundumar Bachi a Ƙaramar Hukumar Riyom ta Jihar Filato.
Rahotanni sun bayyana cewa, ɗalibin, mai suna Badung Sunday Alamba ɗan shekara 29 ya rasu ne a lokacin da maharan suka yi kwanton ɓauna a mashigar ƙauyen, inda suka buɗe wa wasu ‘yan ƙauyen biyu wuta. Ɗaya daga cikinsu ya samu tsira yayin da shi kuma Alamba ya rasa ransa.
An ce shi kaɗai mahaifiyarsa ta haifa, wanda hakan ya jefa iyalansa da ‘yan ƙauyen nasu cikin ƙunci da jimamin rashin sa.
Wani ɗan ƙauyen mai suna Mista Dung Elisha ya tabbatar wa manema labarai faruwar al’amarin, inda ya ƙara da cewa, “Shi ne kaɗai ɗa a wajen mahaifiyarsa.”
Shugaban Ƙungiyar Matasa Maƙera ta Berom (BYM), Rwang Tengwong ya yi tir da faruwar al’amarin, yana mai zargin maharan da kai wa jama’ar Berom farmaki a ƙauyukan ƙananan hukumomin Riyom, Barkin Ladi da Jos ta Kudu.
Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta gudanar da bincike mai zurfi akan al’amarin tare da kamo waɗanda suke da hannu a ciki domin gurfanar da su a gaban doka.
