Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Masu Ruwa da tsaki a babbar jam’iyyar adawa ta ADC a Jihar Katsina sun gudanar da babban taro na ƙara faɗaɗa shugabancin da zai samar da sabbin shugabannin jam’iyyar a matakin jiha da na ƙananan hukumomi da mazaɓu.
Shugaban masu ruwa da tsaki na ADC a Jihar Katsina, tsohon Minista Alhaji Lawal Ɓatagarawa ya bayyana cewa sun kira wannan taro ne domin sanar da magoya bayan jam’iyyar ADC da ke fadin Jihar Katsina, cewa jam’iyyar ta ƙasa ta umarci jihohi cewa a ƙara faɗaɗa shugabancin jam’iyyar a matakin jihar da ƙananan hukumomi 34 da ke jihar.
Alhaji Lawal Ɓatagarawa ya ƙara da cewa babban dalilin da ya sanya suka ɗauki wannan Shawara na ƙara faɗaɗa wannan shugabanci shine domin a ƙara bada dama ga waɗansu muhimman mutane da ke ta ahigowa cikin jam’iyyar ta ADC.
A jawabin sa jagoran jam’iyyar ADC na Jihar Katsina Dakta Mustapha Muhammad Inuwa ya yi kira ga ɗaukacin shuwagabanni da magoya bayan wannan jam’iyya ta ADC a Jihar Katsina da su cigaba da haƙuri da haɗa kawunan su domin samun nasarar jam’iyya ta ADC a nan Jihar Katsina da ma ƙasa baki ɗaya.
Shima tsohon Sanata a Shiyyar Daura Sanata Ahmed Babba Kaita ya yabawa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ADC a jihar Katsina bisa irin haɗin kai da goyan bayan da kowa yake badawa domin ganin jam’iyyar ADC ta samu nasara a kowane mataki.
Tsohon ɗan majalissar taraiya wanda ya wakilci ƙananan hukumomin Malumfashi da Kafur, Hon. Babangida Talau Malumfashi ya tabbatar wa ya’yan jam’iyar a wannan taro cewa wannan zaɓe da za’a gudanar za’ayi shi ne ta hanyar sasanci kamar yadda uwar jam’iyyar ADC ta ƙasa ta basu umarni.
