Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Wata babban kotu da ke zaune a Katsina ta dakatar da duk wata hidimar jam’iyar ADC har zuwa 15 ga wannan wata da za ta saurari ƙara da shugaban jam’iyar Alhaji Usman Wamba ya shigar.
Mai Shari’a A K Tukur ya bada umurnin a ƙarar da shugaban jam’iyar ADC a jihar Alhaji Usman Wamba ya shigar inda ya ke buƙatar dakatar da hidimar jam’iyar a jihar.
Waɗanda ake kara sun hada da Lawal Batagarawa, Babangida Ibrahim Mahuta, Uwar jam’iyar ADC ta ƙasa da hukumar zaɓe ta ƙasa kan wasu buƙatu guda shida.
Kotu ta amince da buƙatar har zuwa ranar 15 ga wannan wata ranar da za ta fara sauraren ƙarar.
Jam’iyar ADC a jihar ta fara shirye-shiryen gudanar da zaɓubbukan a matakin mazaɓu, ƙananan hukumomi da babban taro na jihar sai dai da wannan mataki na kotu komai ya tsaya.
