Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Duba da yadda hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ke ci gaba yi wa ‘yan ƙasa rajistar katin jefa ƙuri’a, ƙungiyar musulmi ta mabiya Shi’a a Nijeriya, wato ‘Ahlul Baiti Nijeriya ta yi kira ga ‘ya’yan ƙungiyar da ba su da katin zaɓe, cewa da su hanzarta yin haka, kasantuwar wajibcin katin a harkokin su na siyasa.
Wannan kiran ya fito ne daga bakin shugaban gamayyar ƙungiyar ta mabiya da masoyan Ahlul Bait (as) ta ƙasa reshen jihar Kano, Hon. Adamu Kabiru (Auduwa) a yayin ganawa da manema labarai a Kano.
Honourable Adamu Kabiru ya ƙara da cewa “Muna kira ga dukkan mabiya da masoyan Ahlul Bait na ƙasar nan da su duƙufa wajen zuwa karɓar katin rijistar zaɓe don samun damar kaɗa ƙuri’a a dukkan matakai na zaɓuka masu zuwa.”
Kazalika ya bayyana cewa duba da irin yawan da muke da shi na mabiya na Ahlul Bait (as) a faɗin ƙasar nan, musamman ganin yanzu aikin yana kan gudana a dukkan ofisoshin zaɓe na dukkan Ƙananan hukumomin 774 da ke faɗin ƙasar nan.
“Zuwa lokacin da za a shiga hada-hadar siyasar ne za a ji matsayarmu na wanda za su kaɗa wa ƙuri’un,
“Za kuma mu zaɓi wanda zai kare mana mutumcin mu da fahimtar mu ta addini, da kuma wasu haƙƙoƙin mu da kowanne ɗan ƙasa ke da shi, wanda kundin tsarin mulkin ƙasar nan ya ba mu.” Inji Hon. Kabiru Auduwa
