
Asusun tallafa wa ilimi (UNICEF) na Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) da Ƙungiyar Ƙasashen Turai (EU) tare da haɗin-gwiwar hukumar illimin bai daya ta Jihar Kano, sun gudanar da taron gangamin wayar da kai game da shirin mayar da yara makarantu a sassan jihar da nufin kawu ƙarshen rashin zuwa makaranta ga yara ƙanana mai taken ‘Education And Youth Empowerment Project in Northern Nigeria’.
Da take jawabin yayin buɗe taron, wanda aka gudanar a makarantar sakandare ta gwamnati da ke Gwammaja a Ƙaramar Hukumar Dala, wakiliyar UNICEF, Hajiya Aisha Abdullahi ta bayyana cewa maƙasudin shirin shine don ƙara ƙarfafa wa iyayen yara, shugabanni ƙungiyoyi da ƙungiyoyin mata gwiwa don ganin yara na shiga makarantu a wannan zangun karatu na shekara ta 2025/2026.
A cewarta dukkan yara sun cancanci zuwa makaranta: “akwai yara da dama da suke ba a makaranta ba saboda rashin wayewa, bukata ta musamman, banbanci jinsi wanda ke kawu raguwar zuwan yara makaranta, wasu kuma wuraran suna fuskantar matsalar barin yaran daga bayan sun fara zawa makarantu.”
Ta ƙara da cewa ƙungiyoyi na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen shawo kan matsalar, “idan aka samu hadin kai tsakanin ƙungiyoyi da gwamnati hakan zai mutukar taimakawa wajen kara wayar da kan alumma musammam iyayen yara, masu kula da su wajen ganin ana sanya idanu don ganin suna zuwa makarantar akan lokacin kuma a kowace rana.”
“Da ma hada kai da ƙungiyoyi, iyaye da malamai na makarantu, kungiyoyin mata dana masu bukata ta musammam da nufin farfadu da harkar illimi a kasar nan musammam bangaran Arewacen kasar nan wanda ake ganin shine koma-baya a fannin ilimi.”
A nasa jawabin, wakilin Arewa, Alhaji Dalhatu Jibrin ya yi godiya ga ƙungiyoyin ƙasashen wajen ganin yadda suke tiri-tiri don ganin illimi ya farfaɗu a ƙasar nan.
Da yake tufa albarkacin bakinsa Shugaban majalisar kansilolin karamar hukumar Dala, Hon. Auwalu Ibrahim Shuaibu nuna farin cikinsu yayi tare da gode wa waɗannan ƙungiyoyi ganin yadda suke tallafa wa fannin illimi a wannan jaha.
