Daga MUKHTAR A. HALLIRU TAMBUWAL a Sakkwato
Ƙungiyar Mata Masu Karɓar Zakka da Waƙafi ta yi rabon zakkar kuɗi ga mata masu ƙananan sana’oi su 20 da aka zaɓo su daga wasu makarantun Islamiyya, domin su dogara da kansu.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyar ta gudanar da wani shirin wayar da kan matan akan muhimmacin bayar da zakka, da kuma kasancewa daga masu karɓar zakka zuwa masu bayar da ita.
A cewar shugabar ƙungiyar, Malama Amina Musa Sakaba, sun fito da wannan shirin ne domin tallafawa mata masu ƙananan sana’oi, domin su dogara da kansu, ta yadda zai kasance za su iya karɓar zakkar su ma watarana sun zama masu fitar da zakkar.
Shugaban Hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Sakkwato (SOZEA), Malam Muhammad Lawal Maidoki, shi ne ya ƙaddamar da rabon Zakkar a ɗakin taro na Cibiyar IET da ke Sakkwato.
Kowacce daga cikin matan su 20 ta samu Naira dubu 50 a matsayin Zakka, domin ƙara haɓaka kasuwancinsu. An kuma faɗakar da su dabarun tattalin kuɗi da kasuwanci ta yadda kasuwancin na su zai ɗore.
Wasu da aka zanta da su sun yi godiya tare da ba da tabbacin yin amfani da abin da aka basu kamar yadda aka nema.
