Ƙungiyar WICE ta karrama Dakta Amina

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Ƙungiyar Mata Malaman Kwalejin Ilimi na gwamnatin Tarayya ta ‘National Association of Women in Colleges of Education’ (WICE) ta karrama Hajiya Dakta Amina Haruna Abdul, ƙwararriyar Malama a Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya FCE da lambar yabo.

Dakta Amina ita ce Wakiliyar Tula, ta farko ƙungiyar WICE ta karrama ta bisa da lambar Yabo bisa ayyukan jinƙai da taimakon al’umma da ta ke yi ako yaushe wajen ganin ta inganta ilimin ‘ya’ya mata.

An karrama ta a wani taron da ƙungiyar ta na ƙasa da suka gudanar a Kwalejin Ilimi na gwamnatin Tarayya ta FCE da ke Okene, a babban taron ta da ta gudanar.

A zantawar ta manema labarai a Gombe bayan wannan karanci  da aka yi ma ta inda ta ce tana cike farin cikin, inda ta godewa Allah da ƙungiyar WICE na yadda suka ga ayyukan Alkairi da take yi har aka mata wannan karamci.

Dakta Amina Abdul, ta ƙara da cewa, an ba ta lambar yabon ne bisa wasu ayyukan taimakon al’umma da jin kai wa marasa galihu musamman ‘ya’ya mata da ba su da galihu.

Har ila yau ta ce ta daɗe tana bada guduwar ta wajen ceto rayuwar al’umma musamman a wannan zamani da komai ya taɓarɓare wajen ganin ta samar wa da mata ’yancin su musamman a ɓangaren samar da ilimin zamani.

Sannan ta yi amfani da wannan damar ta yi kira ga shugabanin ƙungiyar su ta WICE da su ci gaba da zaƙulo wasu matan ana karrama su don ƙara musu ƙwarin gwiwa.

Daga nan sai ta ce, aikin jin ƙai kuma a jininta ne ya ke, inda yanzu ne ma ta fara, sai lokacin da Allah ya ɗauki kwanan ta.