Shawarwari ga matasa masu shirin aure (1)

Assalamu alaikum, da sunan Allah mai rahama mai kin ƙai. Da farko dai yana da kyau a fahimci cewa ɗaura aure yana nufin ƙulla wata alaƙa ce da Ubangiji Maɗaukakin Sarki ya yi umarni da ita. Gaskiya ne cewa (aure) ya kasance daga cikin ɗabi’u na ɗan Adam, to amma duk da hakan Allah Maɗaukakin Sarki ya tsarkake wannan alaƙa wacce daga ƙarshe take haifar da abubuwa masu kyau. Don haka bai kamata a ɗauki wannan alaƙa a matsayin wani abu mara muhimmanci ba.

Ɗaya daga cikin munanan ayyukan da wasu suka yi shi ne riƙon sakainar kashin da suke yi wa wannan alaƙa da rashin ba ta muhimmancin da ya kamace ta. Su dai turawa suna mu’amala ne da wannan muhimmin lamari, wannan wata alaƙa ce mai ƙarfi tsakanin mace da namiji, mu’amala tamkar ta cire riga ko kuma shiga wani shago, wato a matsayin wani abu kawai mai sauƙi kana iya yinsa yanzu ka kuma canja shi duk lokacin da ka ga dama. Don haka wannan aƙida ta kan sanya shu’uri da ɗanɗanon mutum su kasance masu adawa da ci gaban wannan alaƙa ta auratayya.

A duk lokacin da ɗaya ɓangaren (macen ko namijin) ya ga wani abu ko kuma suka fuskanci wata matsala, to ba tare da haƙuri da la’akari da wasu abubuwa ba akan kawo ƙarshen wannan alaƙa (mai tsarki). Amma shi kuwa addinin Musulunci bai yarda da hakan ba, (wato baya kwaɗaitar da hakan) don kuwa a Musulunci an gina tushen iyali ne bisa ƙarfafan tubalai. A koda yaushe Musulunci ya kan ja kunnen mabiyansa wajen yin taka-tsantsan a lokacin da suke ƙoƙarin zaɓen abokin zama ko kuwa abokiyar zama sannan da kuma yin duk abin da mutum zai iya wajen kiyaye wanzuwar wannan tsarkakakkiyar alaƙa. Dole ne ku yi iyakacin ƙoƙarinku wajen kare wannan sabuwar alaƙa, kamar yadda kuke kula da sabbin tsirran da kuka shuka don su girma su zama bishiyar da za ku amfana da ‘ya’yanta.

Yana da kyau a fahimci cewa, kula da wannan alaƙa ba ta na nufin irin kuɗin shigan da mutum yake samu, ko kuma yawan ilminsa ko kuma irin aikin da yake yi kawai ba, don kuwa shu’urin ɗan Adam kan aure da gina iyali kusan abu guda ne, babu wani gagarumin bambanci tsakanin masani, malami, ɗan wasa, ko kuma lebura da dai sauransu, hakan kuwa saboda shu’urin guda ne tsakankanin dukkan mutane, babu wani bambanci tsakanin talaƙa da mai kuɗi.

Babu shakka kowani guda daga cikin miji da mata suna son gidansu ya kasance wajen kwanciyar hankali da nitsuwa gare su bayan sun gama aikace-aikacensu na rana, wannan wata buƙatuwa ce da ma’auratan suke buƙatuwa da ita a rayuwarsu ta aure; suna buƙatuwa da farin ciki da yanayin da yake samar da hakan. Mai yiyuwa ne (macen ko namijin) su kasance ‘yan kasuwa, ko kuma ‘yan siyasa ko kuma suna zama ne a gida don tarbiyyantar da yara, kai ko ma dai wani irin aiki suke yi, dukkansu sukan gaji, to a lokacin da suka dawo gida, suna buƙatar yanayin cikin gida mai faranta rai, wannan kuwa ba wata buƙata ce ta wuce guri ba, a’a, a ɗabi’ance haka lamarin yake.

Haƙiƙa lamarin ba shi da alaƙa da abin hannun da mutum ya ke da shi, don kuwa akwai da dama daga cikin masu abin hannun da ba su ɗanɗani daɗin zamantakewar aure ba, rayuwarsu ta kasance cikin ƙunci, cike take da hassada da haramtattun buƙatu da fata. Babu shakka mutumin da ke da wani mukami, wanda yake ba da umarni, ya kan iya fuskantar matsaloli daban-daban a gida, me yiyuwa ne shi wannan mutum ko kuma wannan matan ya/ta samu abokin zama mai saurin fushi, mara haƙuri ko kuma malalaci. Don haka dukiya, mukami, zaman birni ko ƙauye ba za su canja yanayin zamantakewar iyalai ba matuƙar dai babu fahimtar juna da yafewa tsakanin ma’auratan biyu. Don haka ne ma Allah Maɗaukakin Sarki cikin Alƙur’ani mai girma yake cewa:

“Shi ne Wanda Ya halicce ku daga rai guda, Ya kuma halicci matarsa daga jikinsa don ya sami nitsuwa da ita…” (Suratul A’araf 7:189). Abin da Alƙur’ani yake nufi shi ne ‘mu’amala da juna cikin ƙauna da kuma samun kwanciyar hankali da juna’. Lalle ya kamata mata da miji su kasance hanyar zaman lafiya, kwanciyar hankali da ƙauna tsakanin junansu, don haka dole ne ya ku matasa maza da mata ku sanya hakan cikin zukatanku, don kuwa aurenku zai kasance sanadiyyar haifar da iyali. Dole ne gidan da za ku zauna ya kasance waje ne na kwanciyar hankali da nitsuwa gare ku da kuma ‘ya’yan da za ku haifa. A tare mu a mako na gaba. Wassalam.

Daga Mustapha Musa Muhammad a Kaduna, 08168716583.

Rikici a jam’iyyun APC da PDP

Talakawa a yi hattara domin kuwa a makonni biyu baya ne aka gudanar da wasu zaɓuka na fitar da muƙamai a jam’iyyun APC mai mulki da PDP mai adawa, inda ga alamu aka samu a wasu Jihohi kamar Kano an yi zaɓe amma ɓangarori biyu wanda baya ga na ɓangaren mai girma gwamna wanda a ka ayyana shugaba Jam’iyyar APC na riƙo, Alhaji Abdullahi Abbas a matsayi sabon shugaba da a ka zaɓa a gefe guda an jiyu cewa a nasu ɓangare na Sanata Ibrahim Shekarau ɗan takarar su Alhaji Haruna Danzago ne wanda su ka sanar sun zaɓa.

A can Jihar Bauchi ma an samu ɓangarori ma su ja-in-ja duka a ita Jam’iyyar ta APC. Ita kuma Babbar Jam’iyya mai adawa PDP babban ƙalubale da ta ke cigaba da fuskantarsu magana ce ta shugabanci duk da an zaɓi Mr Auyo, amma a rahoton BBC Hausa na ranar 15 ga Oktoba, 2021, mun ji cewa da sauran rina a kaba! Wasu sun ce sai a mayar wa tsohon Shugaba Mr Uche, wanda hakan ke fiddo wata matsalai. Shawara ga talakawa; a nutsu a duba cancanta kafin zaɓen 2023.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa. 07066434519

Rayuwar gidan haya

Ina magana ne daga jiharmu, Jihar Katsina, domin a shekaru 30 zuwa sama duk wanda zai yi aure ba zai bazama neman gida ko ɗakin haya kamar a yau ba. Na samu kaina a zaman haya daga shekarar 2000 zuwa 2002 wanda kafin in mallaki nawa gidan na fuskanci yadda rayuwar haya ta ke.

Dillalai a kula; haka nan ku waɗanda ke gina gidaje ku ba da haya duka a riqa sanya tausayi da sauƙaƙawa. Mutum ne zai zo neman gida ko ɗaki na haya za a gindaya masa wasu sharuɗɗa duka ya cika kuma kuɗi ya bada amma idan an damƙa masa makullai zai taras gidan na da buƙatar gyare-gyare wanda a tsakanin mai gidan da dillalin gidan duka sun san da hakan.

Duka sai mun riqa fahimtar idan mun tausaya ma junan mu rayuwa za ta inganta kuma aminci ya yawaita a tsakanin mu. A Katsina akwai wani mutum wanda yana da gidaje na haya amma idan ka amsa kafin ka shiga zai yi gyare-gyare da fanti duka da aljihunsa. Allah ka ba mu ikon gyarawa ta kyautatawa. Ameen.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa Katsina. 07066434519, 08080140820.