Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Ƙungiyar ‘yan jaridar Kano ta Arewa wato Kano North Journalists Forum (KNJF) ta gudanar da babban taronta na farko a ƙaramar hukumar Bichi a ranar Lahadi, da ya samu halartar fitattun ƴan jarida dake aiki a wurare daban-daban na ƙasar nan.
Taron, wanda ya gudana ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar, Comr. Sha’aibu Sani Ɓagwai, inda ya bayyana cewa, manufar shirya taron, ita ce ƙarfafa zumunci, haɗin kai da fahimtar juna tsakanin ƴan jaridar yankin Kano ta Arewa.
Ya ce an kafa ƙungiyar ne don ganin ‘yan jarida sun haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen fitar da matsalolin da al’ummar yankin ke fuskanta, da nufin jawo hankalin mahukunta don ɗaukar matakai masu ma’ana.
Kazalika, Ɓagwai ya ce matsalolin da ake son mayar da hankali a kai sun haɗa da tsaro, ilimi, lafiya, hanyoyi, da kuma noman rani, tare da ƙoƙarin kawo ci gaban da zai inganta rayuwar jama’ar a yankin.
“Mun ƙuduri aniyar amfani da ƙarfin kafafen watsa labarai wajen haskaka matsalolin jama’a, domin a ɗauki matakin da zai kawo sauyi mai ɗorewa,” in ji Ɓagwai.
Shi ma a jawabinsa, Dattijo a aikin jarida Ibrahim Nageda Bichi ya bayyana cewa babban abinda aikin jarida ya ke buƙata shi ne shi tsayawa kan gaskiya, jajircewa da kuma aiki tuƙuru.
“Abinda aka san ɗan jarida shi ne duk wani wuri da ake zaluntar marasa ƙarfi ko ake tauyewa wani haƙƙi, idan ɗan jarida bai iya nemo wa ba to wane ne zai iya nemowa? Inji Nageda.
Taron dai ya samu halartar tsoffin ‘yan jarida da dama na wannan yanki Kano ta Arewa da ke aiki a manyan kafafen yaɗa labarai a faɗin ƙasar nan, waɗanda suka yaba da wannan sabon yunƙuri na haɗa kai da ƙarfafa cigaban aikin jarida.
