
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙaramin Ministan Ayyuka, Bello Goronyo ya bayyana kaɗuwarsa akan ayyukan zagon-ƙasa da ake yi wa aikin babban titin Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano.
Goronyo ya faɗi haka ne a yayin sanya ido a wani sashi na aikin a jiya Asabar, inda ya kirayi jagororin al’umma da su yi jan hankali ga waɗanda suke jagoranta akan munanan ayyukan.
Ya ce, waɗanda aka bai wa kwangilar aikin suna iya bakin ƙoƙarinsu ba dare ba rana wajen ganin sun yi aiki mai kyau don haka ba daidai ba ne ace wasu na ɓatawa.
Ministan ya bayyana cewa sun gano cewa mutane su kan je cikin dare su yi ta farfasa wani sashe na hanyar tare da cire rodi aka sa domin ƙarfafa aikin da aka yi.
Haka kuma ya ce an samu wasu ɓata-gari sun je cire rodunan da aka sanya wa Gadar Jaji a Kaduna, yayin da wasu kuma ke busar da kayan hatsi da zubar da shara akan titi.
Ya yi tir da hakan inda ya kira ga jagorori da ɗaukacin al’umma da su sanya ido wajen ƙalubalantar masu ire-iren ayyukan domin tabbatar barin hanyar bisa inganci ga zirga-zirgar al’umma.
