
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce za ta ɗauki ƙarin wasu jami’an lafiya guda 9,000 a jihar daga yanzu zuwa nan da shekara biyar masu zuwa.
Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Ahmed Maiyaƙi ya bayyana haka a yau Lahadi a Kaduna, yayin wani zama na kwana ɗaya da ya ƙunshi harkar labarai, wanda Hukumar Ci-gaban Insorar Lafiya ta jihar (KADCHMA) da haɗin-gwiwar ƙungiyar lafiya mai zaman kanta, wato Lafiya: UK-Nijeriya Partnership for a Healthier Future’ suka jagoranta.
Ya ce, a kwanan nan ne Gwamna Uba Sani na jihar ya amince da ɗaukar ma’aikatan lafiya su guda 1,800 a matakai daban-daban da nufin inganta harkar lafiya a faɗin jihar.
Kwamishinan ya ƙara da cewa tun a 2023 da gwamna Uba Sani ya kama mulki, ya ke fifita harkar lafiya har zuwa yau domin amfanin al’ummar jihar.
A cewarsa, gwamnan ya kuma inganta albashin ma’aikatan lafiya, wanda hakan ke faɗaɗa matakin walwalarsu, lamarin da ya sa jami’an lafiya da dama ke koma wa aiki a jihar.
A ƙarshe, Kwamishinan ya roƙi ƴan jarida da su riƙa ƙoƙarin wayar da ƴan jihar da ke shirin aiki a fannin lafiya akan yadda gwamnatin jihar ke inganta shi.
