Ɓatar yara a Borno na ƙaruwa yayin da ake zargin Boko Haram da ɗaukar sabbin mayaƙa 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Batun ɓatan yara a Jihar Borno ya fara tayar da hankalin jama’a, bayan wani bidiyo ya fito ya na nuna wani yaro na furta cewa ana ba shi horo na soja a cikin daji tare da wasu yara da dama.

Wasu mazauna yankin da su ka zanta da The Punch a ranar Lahadi sun bayyana damuwarsu game da damuwa da su ke fuskanta na rashin sanin inda ‘yan uwansu su ke, tare da fargabar cewa karuwar yawan ɓatan yara a jihar na iya alaka da yunƙurin mayar da su ‘yan ta’adda.

Wani faifan bidiyo na wani yaro mai kimanin shekara 10 da haihuwa da ya bayyana yana karɓar horo kan amfani da makamai tare da wasu yara kusan 30 a cikin dajin Ajiri da ke ƙaramar hukumar Mafa a Jihar Borno, ya karaɗe kafafen sada zumunta a ƙarshen mako.

Bidiyon, wanda wani mai suna Zagazola Makama ya wallafa a shafin ɗ kuma aka ce an ɗauke shi a ranar 22 ga Janairu, 2025, ya nuna yaron yana ƙoƙarin nuna yadda ake sarrafa bindiga.

Ya bayyana cewa shi da sauran yara ana ba su horo a cikin daji mai zurfi.

Wasu mazauna yankin sun bayyana damuwarsu kan yadda ake fama da yawaitar ɓatan yara a jihar, lamarin da suke tunanin yana da nasaba da bidiyon da ya karaɗe intanet.

Aisha Ali, wata mazauniyar Mafa, wadda ke kusa da dajin da ake zargin ana bautar da yaran, ta tabbatar da cewa ɗanta mai shekara shida ya ɓace tsawon shekaru uku ba tare da an same shi ba.

Da Punch ta tuntuɓi rundunar ‘yan sanda ta jihar Borno, kakakin rundunar, Nahum Daso, ya ce ana samun rahoton ɓatan yara aƙalla sau ɗaya a kowane mako.

Sai dai a kan bidiyon, Daso ya ce ana iya amfani da tsofaffin bidiyo domin tayar da hankali.

By ukarofi