Ɗalibai 91 sun kammala haddar Alƙur’ani a makarantar Aƙsat a Gombe

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Makarantar Aƙsat da ke Gombe ta kammala yaye ɗalibai 91, ciki har da matan aure guda takwas, a bikin yaye ɗaliban ta karo na goma. 

Wannan makaranta, wacce aka kafa a shekarar 2009, ta riga ta yaye mahaddatan Alƙur’ani guda 600 tun daga lokacin da ta fara.

A cikin bikin, shugaban ƙaramar hukumar Gombe, Barista Sani A.A Haruna, ya yaba wa mamallakin makarantar, Dakta Auwal Abdullahi Gafakan Akko, saboda ƙoƙarinsa na yaɗa ilimin Alƙur’ani a jihar. 

Haruna ya kuma yi kira ga Dakta Auwal da ya faɗaɗa makarantar zuwa sauran ƙananan hukumomi 11 na jihar domin ƙara samun mahaddatan Alƙur’ani.

Sani Haruna ya jaddada cewa haddace Alƙur’ani yana buƙatar aiki da koyarwar sa a cikin rayuwa, ya kuma shawarci sabbin mahaddatan da su guji wasan kwaikwayo da abin da suka koya.

Shugaban Kwalejin Islamiyya da Shari’a ta Nafada, Farfesa Safiyanu Ishiaku, ya bayyana damuwarsa kan yadda tarbiyyar al’umma ke raguwa, yana mai buƙatar gwamnatin jihar ta ƙara mayar da hankali wajen tallafa wa irin waɗannan makarantu.

Babban Malami a jihar, Sheikh Adamu Muhammad Dokoro, ya yi tsokaci kan halin tsadar rayuwa, yana mai jaddada muhimmancin juyawa zuwa ga Allah domin samun sauƙi daga wannan yanayi.

Mamallakin makarantar, Dakta Auwal Abdullahi Gafakan Akko, ya gode wa iyaye da suka tura ’ya’yansu makarantar, yana mai bayyana cewa makarantar tana da rassa guda biyar a Gombe, kuma tana shirin faɗaɗa zuwa sauran wurare.

Duk da matsalolin da ake fuskanta na tsadar rayuwa, iyaye da ɗalibai sun ci gaba da goyon bayan makarantar domin ci gaban ilimin Alƙur’ani mai girma a jihar Gombe.

By ukarofi