Ɗan canji ya danganta Saleh Mamman da almundahanar biliyan N33.8

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani ɗan kasuwar canjin kuɗi ya ce, ya karɓi sama da Naira Biliyan 22 daga Ma’aikatar Wutar Lantarki ta Tarayya, wanda hakan ya sanya ma’aikatar cikin almundahanar Naira Biliyan 33.8.

Hakan ya fito fili ne lokacin da ake shari’ar Saleh Mamman, tsohon ministan wutar lantarki a babbar kotun tarayya da ke Abuja.

A ranar Laraba ne aka ci gaba da shari’ar da James Omotosho ya jagoranta, inda Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta gabatar da shaida ma takwas, Abdullahi Suleman, wanda shi ne ma’aikacin BDC.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Dele Odewale, shugaban yaɗa labarai na EFCC.

A cewar sanarwar, Suleman ya bayyana yadda aka fitar da sama da Naira Biliyan 22 daga ma’aikatar a lokacin da Mamman ke kan muƙamin.

Ya bayyana cewa an canja kuɗin Naira kwatankwacin dalar Amurka ta hanyar asusun kasuwanci da dama da ke haɗe da shi.

Kamfanonin Suleman da suka haɗa da Prymint Inɓestment Limited, Strong Field International Projects Limited, da wasu da dama, an yi zargin an yi amfani da su wajen gudanar da hada-hadar ba tare da aiwatar da kwangila a hukumance ba.

A cewar Suleman, an shigar da kuɗaɗen ne cikin asusu 12 na kamfanonin sa, da kuma wani asusu mallakin kamfanin ɗan uwansa, Gurupche Business Enterprises.

“Daga ƙididdigar da na yi, adadin da na samu ta hanyar hada-hadar kuɗi ya haura biliyan N22,” ya shaida wa kotu.

Suleman ya kuma bayyana mu’amalarsa da wani mai suna Maina Goje, wanda shi ne ke haɗa hada-hadar kasuwanci tare da ba shi umarni kan canja kuɗi zuwa dala.

Suleman ya yi zargin cewa wani mutum ne da ake yi wa laƙabi da “Yaro Minister” ke wakilta Goje, wanda aka ruwaito cewa makusanci ne ga Saleh Mamman.

By ukarofi