Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD
Wata babbar kotun tarayya da ke Maitama a ranar Alhamis ɗin da ta gabata shaida cewa Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika ya amince da bayar da kwangiloli ga wani kamfani mai suna Al Buraƙ Global Inɓestment Limited wanda ɗiyarsa, Fatima Hadi Sirika da mijinta Jalal Sule Hamma ke jagoranta.
An ruwaito cewa, wani tsohon darakta mai kula da sayar da kayayyaki a ma’aikatar sufurin jiragen sama, Musa Odiniyan ya bayyana haka a lokacin da yake ba da shaida a ranar Alhamis a matsayin mai gabatar da ƙara na biyar a ci gaba da shari’ar Sirika, Fatima, Jalal da Al Buraƙ Global kan tuhume-tuhume shida na munanan ayyuka.
A cikin tuhume-tuhumen, masu gabatar da ƙara sun yi zargin cewa Sirika ya yi amfani da matsayinsa wajen bai wa Al Buraƙ Global Inɓestment Limited damar da ba ta dace ba, wanda ɗiyarsa Fatima Hadi Sirika da mijinta Jalal Sule Hamma ke jagoranta, ta hanyar ba da kwangilar Eɗtension na Apron a filin jirgin sama na Katsina akan kuɗi N1,498,300,750.”
An ce Fatima ma’aikaciyar kamfanin man fetur ta Nijeriya ce, yayin da Jalal Sule Hamma aka bayyana ma’aikacin Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya.
A ranar Alhamis, Odiniyan, yayin da lauyan Sirika, Michael Numa (SAN) ke yi masa tambayoyi, ya dage cewa kafin a aiwatar da kwangilar, ministan ya amince.
“Ministan shi ne mutum na ƙarshe da ya amince da bayar da kwangilar. Dole ne ministan ya amince da hukuncin kwamitin bayar da kwangilar ministocin kafin a aiwatar da kwangilar,” inji shi.
