Nijeriya za ta jagoranci bunƙasa Afirka a fannin ilimi da noma – Shettima

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ce sadaukarwar da Nijeriya ta yi na amfani da ƙarfin matasanta, da saka hannun jari a fannin ilimi, da inganta aikin noma, dabaru ne da suka dace da za su taka rawar gani wajen tunkarar ƙalubalen duniya ke ciki.

Da yake magana a taron tattalin arzikin duniya na ‘Financial Times Global Risk Roundtable’ a ci gaba da taron tattalin arzikin duniya na 2025 (WEF) a birnin Daɓos na ƙasar Switzerland, mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa, matasan Afirka ne kan gaba wajen kawo sauyi.

Mataimakin shugaban ƙasar ya ce duk da cewa akwai ƙalubale da dama, amma hakan na nuna irin jajircewar da al’umma za su iya yi ne.

“Eh, muna da ƙalubale, amma waɗannan ƙalubalen kai mu ga inganta al’ummarmu da kuma gina al’umma nagari ne,” inji shi.

Mataimakin shugaban ƙasar ya sake jaddada aniyar Nijeriya na rungumar ƙirƙire-ƙirƙire da ƙarfafa gwiwa, musamman ta hanyar ilimi, dabarun da suka shafi jinsi, da aikin noma na zamani don ciyar da tattalin arzikinta zuwa karo na huɗu bayan juyin juya halin masana’antu.

“ƙalubalen ya ba mu dama ta musamman na saka hannun jari ga mutane, musamman a fannonin da za su ba mu damar daidaita tattalin arzikinmu zuwa gasa a duniya,” inji shi.

Ya kuma nuna rashin amincewa da dogaro da tallafin da ƙasashen ƙetare ke bayarwa, inda ya bayar da shawarar a yi haɗin gwiwa daidai gwargwado da zai kare mutunci.

Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana kyakkyawan fata game da makomar Afirka, tare da lura da albarkatu masu tarin yawa da muhimmancin dabarun ci gaban duniya.

Ya yi kira da a samar da haɗin gwiwa tsakanin ɓangarori daban-daban, yana mai jaddada cewa, dangantakar da ke tsakanin ƙalubalen duniya na buƙatar mafita ta haɗin gwiwa.

Shettima ya bayyana yadda ake samun bunƙasar saka hannun jari a ƙasar inda ya roƙi masu zuba jarin da su yi watsi da labaran ƙanzon-kurege da ake yaɗawa kan rashin tsaron dukiyoyin masu zuba Jari a Nijeriya 

Mataimakin ya ce a yanzu Nijeriya na hannun ƙwararru duba da matsayin shugaban ƙasar na gogaggen masani a kan kasuwanci.

Mataimakin shugaban ƙasar ya jaddada irin ƙarfin da nahiyar Afirka ke da shi, inda ya bayyana cewa nahiyar ta farka kuma a shirye ta ke ta ɗauki matsayinta a duniya yana mai ambato kalaman marigayi shugaban Nijeriya, Janar Murtala Mohammed, inda yake cewa Afirka dattijiyar nahiya ce da ba ta cancanci a sanya ta a sahun matasan Nahiyoyi ba.

Jim ƙaɗan bayan kammala tallata Nijeriya da Afirka a matsayin wuraren zuba jari, Kashim Shettima ya halarci wani zaman da wasu shugabannin ƙasashen Afirka da suka haɗa da shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa da shugaban Botswana Duma Boko, zaman na su ya biyo bayan buƙatar ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin ƙasashen Afirka da haɗin gwiwar tattalin arziki.

By ukarofi