
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sakamakon bidiyon fasinjar Ibom Air, Comfort Emmanson da ya karaɗe shafukan sadarwa, wani babban ɗan kasuwa ya sanar da ba ta kyautuka ciki har da iPhone 16 Pro Max.
Conform ta tsinci kan ne a mawuyacin hali bayan tsama da wata ma’aikaciyar kamfanin Ibom Air a filin jiragen sama, al’amarin da ya kai ga an tsare ta a gidan gyaran hali na Kirikiri duk da an sako ta daga baya.
Akan haka wani ɗan kasuwa mai suna Ubong Bassey ya ci alwashin bai wa Comfort irin wayar iPhone ɗin ta ce ta rasa yayin faruwar al’amarin.
Haka kuma, hamshaƙin, wanda ake kira da Oga Uby a Facebook ya ce zai ba ta aikin jakadanci na shekara huɗu a wani kamfaninsa.
Tuni ya shaida wa jaridar Legit.ng cewa kamfanin nasa ne kuma har ya fara tattaunawa da Comfort, kamar yadda ya wallafa a kafar sadarwa.
