Ɗan Majalisar Jihar Zamfara ya sha kashi a hannun al’ummar sa

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Ɗan Majalisar Jihar Zamfara mai wakiltar ƙaramar hukumar Maru ta Kudu, Hon. Kabiru Mika’ilu Dangulbi yasha dukan tsiya a hannun al’ummar sa a Garin Dansadau da ke ƙaramar hukumar Maru.

Rahotanni sun bayyana cewar lamarin ya faru ne a jiya Laraba yayin da ɗan majalisar ya bi tawagar gwamnan jihar a yayin da gwamna Dauda Lawal ya kai ziyarar aiki a yankin na Dansadau.

Ɗan Majalisar ya fuskanci fushin al’ummar sa ne a yayin da ya fito wajen jim kaɗan bayan Gwamna Dauda Lawal ya shiga fadar sarkin na Dansadau don ganawa da shi.

Fusatattun matasan sun koka bisa yadda ɗan majalisar ya yi watsi da al’ummar sa tsawon shekaru biyu ba tare da kai masu ziyara ba, musamman kasancewa sunfi ko wane yanki a ƙaramar hukumar ta Maru fuskantatar matsalar rashin tsaro.

Wani mazaunin yankin Muhammadu Lawali Dangulbi, ya bayyanawa wakilin mu cewar tun zaɓen Hon Kabiru Mika’ilu Dangulbi, bai taba zuwa ko ya kira waya don jajanta masu ba akan matsalar rashin tsaro a yankin.

Ya bayyana matakin da matasan yankin suka ɗauka a kansa a matsayin abunda ya dace, yana mai nuni da cewar matakin zai zamo gargaɗi ga mambobin majalisar dokokin jihar da masu riƙe da muƙaman siyasa.

Majiyar mu ta tattaro cewar tuni aka garzaya da Hon. Kabiru Mika’ilu Dangulbi wani asibiti a Gusau don kulawa da lafiyar sa bayan dukan da ya sha a hannun al’ummar sa, wanda ya haifar mashi da bugun zuciya.

By ukarofi