Za mu biya kansilolin NNPP haƙƙoƙinsu bayan zaɓen 2027 kamar yadda Gwamna Abba ya biya mu, inji Ƙungiyar Kansilolin APC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar kansilolin Jam’iyyar APC ta ƙasa (NPCF) ƙarƙashin jagorancin Hon. Muslihu Yusuf Ali, ta sha alwashin rama wa kura aniyarta wajen biyan kansilolin Jam’iyyar NNPP haƙƙoƙinsu bayan sun lashe zaɓen gwamnan Kano a 2027, kamar yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya biya su nasu haƙƙoƙin.

A cikin wata sanarwa, Hon. Misluhu ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano bisa biyan kuɗaɗen tsofaffin kansiloli a jihar.

Haka kuma, NPCF ta jinjina wa tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje akan ba su damar riƙe muƙamin yayin da yake mulki.

A cewar Hon. Yusuf Ali, yayin da gwamnatin APC ta samu kafuwa a 2027 a jihar, za ta yi irin yadda Abba ya yi wajen sauke nauyin haƙƙoƙin kansilolin yanzu.

“Mun gode wa Gwamna Abba da biyan mu haƙƙoƙinmu, amma godiya ta musamman ga Ganduje, domin shine ya ba mu dama muka zama kansiloli.”

“Mun yi wa Abba alƙawari, insha Allahu a 2027 gwamnatin APC za ta biya haƙƙin kansilolinsa da zai bari na NNPP,” inji Mislihu Alu.

Gwamnatin Jihar Kano ta yi wannan hoɓɓasa ne bayan tsawon lokaci tsofaffin kansiloli suna jiran a biya su haƙƙoƙinsu da aka yi musu alƙawari tun lokacin da suka fara aiki a zamanin tsohuwar gwamnati ta Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

By Babaji