
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar Kotun da ke zaune a Jihar Delta ta fitar da umarnin hana Sufeto Janar na ƴan sanda (IGP) da Hukumar ƴan sanda komawa tilasta wa masu ababen hawa bin dokar amfani da gilashi mai duhu a faɗin Nijeriya.
Mai Shari’a Joe Egwu a ranar Laraba yayin gabatar da umarnin, ya kuma haramta wa ƴan sanda cin mutunci, kamawa ko tatsar masu ababen hawa kuɗaɗe akan al’amarin.
Kotun ta ce, umarnin zai cigaba da aiki ne daga yanzu har sai zuwa lokacin da za a gudanar da shari’ar da aka shigar akan batun.
Hakan na zuwa ne bayan da wani mai suna Mista Israel Joe ta lauyansa Kunle Edun ya shigar da ƙara a jihar bisa matakin da hukumar ta ɗauka na aiwatar da dokar.
A ranar Litinin ne kakakin rundunar ƴan sanda, Benjamin Hundeyin ya sanar komawa amfani da dokar, wadda da za ta fara aiki a ranar 2 ga watan Junairun 2026.
Tuni kotun ta ayyana ranar 24 ga watan Disambar 2025 domin sake sauraron ƙarar al’amarin.
