
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Burkina Faso ta sako sojojin sama na Nijeriya (NAF) guda 11 da ke hannunta, kwana tara bayan tsare su.
Hakan na zuwa ne sakamakon shiga tattaunawa ta difulomasiyya da gwamnatin Nijeriya ta yi tsakaninta da hukumomin ƙasar.
Tawagar Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Ministan Harkokin Waje Yusuf Tuggar ta samu tattaunawa da wakilan ƙasar ƙarƙashin jagorancin Shugaba Ibrahim Traoré na ƙasar a Birnin Ouagadougou.
Da yake jawabin bayan ganawar, Minista Tuggar ya ce Nijeriya da Burkina Faso suna da kyakkyawar alaƙa a tsakaninsu musamman bisa la’akari da haɗuwa akan muhimman al’amuran da suka shafi tsaro, wanda ya taimaka wajen ƙara ƙarfin dangantakarsu.
Ya kuma tunatar da saɓa wa dokokin sararin samaniyar ƙasar, wanda Nijeriya ta yi da-na-sanin faruwarsa, yana mai jaddada girmamawa ga ikon ƙasar da ma dokokin sufurin jiragen sama na ƙasa-da-ƙasa.
Haka kuma, Ministan ya nesanta gwamnatin Nijeriya da kalaman wata jam’iyyar siyasa ta Nijeriya na zargin wulaƙanta sojojin Nijeriya a Burkina Faso.
A ƙarshe, ya jinjina wa Shugaba Traoré da gwamnatinsa bisa yadda ya kula da sojojin bisa mutuntawa a lokacin da aka tsare su.


