Daga AISHA ASAS
Motsa jiki wata ɗabi’a ce da har yau ba ta gama zama ‘yar gida a ƙasar Hausa ba. Har a wannan lokacin akwai waɗanda ke kallon sa a layin ɗaya daga cikin gutsiri-tsoma da bature ke rajin karewa tare da ba shi muhimmanci, wanda a wurin su duk rashin aikin yi ne.
Da yawa ba su amince cewa, atisaye na taka muhimmiyar rawa a layifar gangar jikinsu ba. Wannan ne ya sa jaridar Manhaja ta zaƙulu wannan darasin don ya zama wayar da kai ga waɗanda suka jahilce shi, ya kuma ƙara wa masu yi karsashi, sannan ya zama ilimi ga masu neman ƙarin bayyani kansa.
Atisaye ko in ce motsa jiki abu ne da ya zama magani ɗaya mai warkar da cuta goma, domin tasirin sa a jikin ɗan adam mai tarin yawa ne. kusan kowanne ɓangare na lafiya, motsa jiki na taka rawa a cikin sa har ma ta ɓangaren gyara jikin mutum ya yi sheƙi ko kuma ya tsaya a zubi mai kyau. Sannan zai iya zama silar kawo wasu ababe da jiki ke buƙata kamar kaifin basiri, sannan zai iya kawar da wasu da jiki ke neman maraba da su kamar ƙiba ko tumbi.
Da yardar mai dukka, za mu soma da kawo wasu daga cikin alfanun da motsa jiki ke kawo wa jikin ɗan adam, waɗanda jikin ke buƙata.
Motsa jiki na ƙara kaifin basira:
ɗaya daga cikin romon motsa jiki akwai taimaka wa ƙwaƙwalwa wurin daidai ta kanta, tare da wanke ta ta yadda zata fi saurin fahimta da kuma aje karatu ko wasu madangantar sa. Bari na bada misali da yara masu zuwa makaranta, idan mun lura da kyau, za mu ga yaran da ke zuwa makaranta a ƙafa, sun fi yaran da ake kai da abin hawa saurin sakewa, tare da fahimtar karatu sosai. Kuma sukan ɗara su kawo wuta yayin darasi.
Haka ma a ɓangaren tsofaffi, idan ka sa ido, za ka sami mafi yawan tsofafin da suka cika yawo ba kasafai suke saurin manta abubuwa ba, idan ka cire masu fama da cutukan ƙwaƙwalwa masu shafe tunani, kamar cutar Alzheimer (cuta ce da ke hallaka ma’adanar tunanin ɗan Adam, sanadiyyar mutuwar ƙwayoyin halitta na ɓangaren, hakan kan iya sa ruɗani a wurin bambance jiya da yau ko wanda ya shuɗe. Sau da yawa wannan cuta kan yi sanadin manta ababe masu muhimmanci, ciki kuwa hard a ‘ya’ya da iyaye.)
Motsa jiki na ƙara yawan jinin da ke isa ƙwaƙwalwa:
Yayin da ka ke motsa jiki, ɗan aike da ke kai saƙon jiki zuwa ƙwaƙwalwa zai ƙara girma, don haka zai kai jikin wadatacce. Haka zalika, zai iya tasiri wurin halittar wasu ƙwayoyin halitta da ke da matuƙar muhimmanci a lafiyar ƙwaƙwalwa.
Motsa jiki na taimakon matsalar ciwon ƙafa da hannu:
Duk da cewa, an fi ɗora alhakin matsalar ciwon ƙafafu ko hannaye a ƙarancin gishiri a jikin ɗan Adam, wannan ce ke sa, matsalar ta fi yawaita a lokacin zafi, kasancewar yawan zufa da ake yi. Da wannan wasu ke ganin jikin mai fama da matsalar yawan ciwon ƙafa ko hannu (idan ka cire masu matsalar kariyya da makamantansu) ya fi buƙatar yawaita cin gishiri (masu cutukan da ke da matsala da gishiri kamar hawan jini kada ku haye da yawa, zai fi ku fara da tuntuɓar likitansu kafin ku san adadin da ya kamata ku ci, wanda ba zai yi sanadin motsa ciwon ba.)
Duk da haka, motsa jiki na da rawa babba da yake takawa wurin samar da lafiya ga matsalar, idan ka lurawannan matsalar ta fi yawaita, wato lokacin sanyi, za mu gane motsa jiki bai cika samuwa ba a lokutan sanyi.
4. Motsa jiki na sa kyawon fata:
Masana da dama sun yi amanna cewa, atisaye na bada gudunmawa ta fuskar gyaran fata, musamman ma wanda ake yi da sanyin safiya, wato kafin rana ta fara zafi sosai. Baya ga haka, yana tayar da wasu sassa na jiki da suka kwanta, kamar nonon mace idan ya zube, wanda ya tabbata daga bakin masana cewa akwai wani nau’in atisaye da za ta yi da zai tayar da jijiyoyin wurin wanda zai yo sanadin tashin maman nata. da cewa, shi kansa rashin motsa jikin na haifar da ciwon gaɓoɓi ciki har da ƙafa da hannuwa.
Baya ga haka, akwai matsaloli irin na ciwon magamar gaɓoɓi kamar gwiwa da sauransu, masana sun faɗa cewa, ƙafewar ruwan da ke ba wa wurin damar lanƙwasawa ba tare da matsala ba ce ke haifar da wannan ciwo, domin gaɓar zata haɗu da ‘yar’uwarta, waɗanda dukkansu suka kasance ƙashi, haɗuwar ta su kuwa dole su yi zafi. Daga cikin mafita daga matsalar da masana suka faɗa bayan ababen da za su yi don dawowar ruwan, akwai motsa jiki, wanda suka ce tun farko rashin sa na ɗaya daga cikin ummul khaba’isin matsalar. Idan aka yi duba da lokacin da
