Ɗangote ya yaba wa Tinubu bisa umarnin cinikin mai da Naira

Spread the love


Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Shugaban Matatar Mai ta Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya yaba wa Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, bisa bayar da umarnin a riƙa cinikayyar man fetur da kuɗin Naira maimakon Dala.

Ɗangote, wanda ya bayyana haka a ranar Talatar nan lokacin da ya ke ƙaddamar da fara saye da sayarwar fetur daga matatar tasa a Legas, ya ce hakan zai rage buƙatar Dala da kashi 40 cikin 100, inda hakan ke nufin farfaɗowar darajar Naira da sama ma ta daidato a kasuwar shunku.

A yayin da ya ke jawabi ga manema labarai a harabar matatar da ke Legas, babban attajirin ya ce, “Ina mai gode wa al’ummar Nijeriya da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu bisa samar mana da kyakkyawan yanayin da muka samu nasarar cimma kafa sana’ar makamashi, domin bunƙasa da yalwar arziki.

“Ina kuma so na yaba wa Shugaba Tinubu bisa kawo tsarin sayen ɗanyen mai da kuɗn Naira da kuma sayar da tataccen fetur da Naira. Wannan hikima, wacce za ta bai wa Naira daidato a kasuwar shunku kuma ta rage buƙatar da ake da ita ta daloli da kashi 40, inda lamarin zai sa a ita fita daga tsaka mai wuyar da ake ciki.”

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, a watan Yuni na 2024 ne Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da saye da sayarwar mai a cikin gida ta hanyar amfani da kuɗin Naira, domin a rage tsadar tace ɗanyen man fetur a Nijeriya, matakin da masana da ƙwararru da dama suka yaba wa.

By Babaji