Ɗanmajen Musawa ya buƙaci matasa su zama masu kishin ƙasa 

Spread the love

Daga HABU ɗAN SARKI a Jos

Ɗanmajen Musawa kuma shugaban kamfanin ‘yan canji na Zuma Bureau De Change da ke Abuja, Alhaji Usman Khalil Sani Zuma, ya bayyana buƙatar matasa su zama masu kishin kansu da kishin al’ummarsu. 

Ɗanmaje ya yi kiran haka ne yayin da yake ganawa da manema labarai jim kaɗan bayan ganawarsa da Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, yayin ziyarar kwana uku da ya kai garin Jos, babban birnin Jihar Filato, domin halartar bikin cika shekaru 50 da zuwan Shaihu Ibrahim Inyass zuwa Jos, domin bunƙasa zaman lafiya da fahimtar juna. 

Basaraken ya jaddada buƙatar haɗin kai a tsakanin sarakuna, shugabannin al’umma, da masu faɗa a ji, domin ta haka ne za a samar da kyakkyawan tsari da zai ɗora matasa kan turba tagari, a matsayinsu na manyan gobe. Ya ce, matasa su ne jigon kowacce al’umma, kuma waɗanda tasirinsu yake da nasaba ga cigaban da ake samu a ko’ina a duniya. 

Ya ƙalubalanci matasa su tashi tsaye su nemi ilimi, da sana’o’in dogaro da kai, domin su iya riƙe kansu da taimakawa al’ummarsu, saboda tsayawar su akan ƙafafunsu shi ne zai sa su kuɓuta daga sharrin ɓatagarin ‘yan siyasa, da mugayen abokai, masu lalata makomar matasa, da mayar da su ‘yan bangar siyasa. 

Da yake yabawa gudunmawar da Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu yake bayarwa ga cigaban matasa da wayar da kan ‘yan Arewa game da ƙalubalen da ke gaban su, ɗanmajen Musawa ya yi fatan Ubangiji Allah Ya ja kwanan Mai Martaba, Ya ƙara masa ƙwarin gwiwar cigaba da jagoranci nagari da yake yi wa al’ummar Kano da ɗariƙar Tijjaniyya. 

Ya yi wa Sarkin godiya da samun zarafin da ya yi har ya halarci wannan babban taro da ƙungiyar Da’iratu Ahlul Sa’ada ta shirya a Jos, wanda yake maimaita tarihi na ziyarar sati guda da kakansa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na farko ya kawo Jos, domin tarbar babban malamin addinin Musulunci, Shaihu Ibrahim Inyass, shekaru 50 da suka gabata, bisa gayyatar tsohon shugaban Nijeriya Janar Yakubu Gowon.

By ukarofi