
Daga BELLO A. BABAJI
Jami’in hulɗa da jama’a na Kamfanin Raba Wutar lantarki na Ƙasa (TCN) Ndidi Mbah ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a inda ya ce a wani karo maɓarnata sun sake kai wa layin hari.
Kamfanin ya ce tun da misalin ƙarfe 11:43 na daren Laraba layin ya rasa wuta.
Mbah ya ce tuni jami’ansu na reshen Abuja suka garzaya don gudanar da bincike game da lamarin tare gano musabbabin faruwar sa.
Ya ce sun aika jami’ai zuwa yankin waɗanda a halin yanzu su na ƙoƙarin gyara wuraren da aka lalata.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su kasance masu aiko da bayanan sirri da za su taimaka wajen kama waɗanda ke yin irin ayyukan don ƙaurace wa faruwar irin haka a nan gaba.
