
Daga BELLO A. BABAJI
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bai wa masu filaye 762 a Maitama da Cadestral Zone da A10 da su biya kuɗin takardar shaidar mallaka ta CofO daga nan zuwa sati biyu ko kuma a ƙwace su.
Wike ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Kakakinsa, Lere Olayinka ya fitar a ranar Juma’a inda ya ce ba burinsu ba ne ƙwace filayen, saidai sun yi haka ne don tabbatar da biyan kuɗaɗen ƙa’ida ga gwamnati.
A watan Oktoba, 2024 ne aka bai wa masu filaye 3,273 wa’adin sati biyu su biya kuɗaɗen CofO da ake bin su ko kuma doka ta yi aiki akan su inda 2,511 suka bada haɗin-kai.
Kasancewar akwai sauran 762 da ba su cike ƙa’idar ba zuwa yanzu ya sanya Ministan sake ba su makonni biyu don su kauce wa fushin doka.
Hakan na zuwa ne kwana ɗaya bayan Wike ya ƙwace filaye a Abuja na wasu manyan mutane ciki har da na tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari duk da cewa Kakakinsa Garba Shehu ya musanta cewa filin mai gidansa ne aka ƙwace.
Kazalika, Ministan ya yi barazanar ƙwace filayen shugaban marasa rinjaye na Majalisar Wakilai, Kingsley Chinda da na tsoffin shugabannin Majalisar Dattijawa, Iyorchia Ayu da Ameh Ebute da na Mai tsawatarwa na Majalisar Dattawa, Tahir Monguno waɗanda su ma sun shiga sahun waɗanda aka bai wa wa’adin mako biyun.
