Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta Jihar Kano ta bayyana sunayen mutum uku wanda suka lashe gasar gajerun labarai ta 2024.
Waɗanda suka lashe gasar sun haɗa da Danladi Haruna (Zakariyya ) da labarinsa Gadon gida sai da Horo, da Hauwa Shehu da labarinta Bahaushe mai arziki ne da kuma Zubairu Musa Ballannaji da labarinsa mai suna Bahaushiyar Al’ada.
Hukumar ta bayyana ranar 31/12/2024 a matsayin ranar da za ta karrama waɗanda su ka yi nasara a babban ɗakin taro da ke Mumbayya a unguwar Gwammaja, Kano.
