Da Ɗumi-Ɗumi: A karon farko Matawalle ya iso Gusau ziyarar aiki

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

A karon farko tun bayan zamansa Ƙaramin Ministan tsaro, tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Hon. Bello Muhammad Matawalle ya shigo Gusau babban birnin Jihar Zamfara a yau Juma’a domin ziyarar aiki.

Blueprint Manhaja ta tattaro cewa Ministan zai gana da masu ruwa da tsaki da ‘ya’yan jam’iyyar APC a lokacin ziyarar.

Ana kuma sa ran Ministan zai ziyarci mahaifar sa Maradun hedikwatar ƙaramar hukumar Maradun a yayin ziyarar.

Wakilinmu ya ruwaito cewa ɗaruruwan magoya bayan jam’iyyar APC ne suka yi dandazo a gidan Ministan domin nuna goyon baya kan ziyarar tasa.

Cikakken rahoto na tafe…

By ukarofi