2027: ADC ta ɓoye gurin buɗe yaƙin neman zaɓenta na Sakkwato a yau Laraba kan matsalar tsaro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Yayin da ake cigaba da shirye-shiryen zaɓukan 2027, jam’iyyar adawa ta ADC ta sakaye wurin buɗe yaƙin neman zaɓen ɗan takararta na shugaban ƙasa da aka shirya gudanarwa a Sakkwato, wanda zai gudana a yau Laraba, 4 ga Nuwamba, 2026 tana mai nuna damuwarta kan halin tsaro da zargin yunƙurin hargitsa taron a matsayin dalilanta.

Jam’iyyar ta ce, tana ɗaukar matakan kulawa gabanin taron ne domin kada a ɓata mata shiri, biyo bayan waɗansu rahotanni da ke nuna cewa ana shirin hargitsa gangamin, wanda aka shirya gudanarwa a ranar 4 ga Nuwamba.

Wannan na zuwa ne yayin ƙamarin rikicin siyasa a Sakkwato bayan gwamnatin jihar rufe ofishin jam’iyyar na jihar, zarge-zargen kai farmaki kan magoya bayanta da kuma zargin jam’iyya mai mulki APC da shiga harkokinta.

Kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC, Ɗahiru Mai- Shanu a wata hira da wakilinmu ta wayar tarho, ya ce jam’iyyar da samu wajen taro, amma tana jiran amincewar hedikwatarta ta ƙasa gabanin a sanar da jama’a. Ya ce, jam’iyyar ta kuma sanar da ‘yan sanda da hukumar DSS kan rahotannin da ke zargin ana shirin tayar da zaune-tsaye yayin gangamin, inda ya ƙara da cewa hukumomin tsaron sun tabbatar da bayar da gagarumar kariya ga al’umma yayin aiwatar da taron.

Mai-Shanu ya bayyana cewa, tuni dai wasu mambobin jam’iyyar suka garzaya zuwa Sakkwato gabanin taron duk da cewa akwai abin da ya kira da taƙaice masaukin baƙi ga baƙinta daga ɓangaren gwamnatin jihar.

A game da rufe ofishin jam’iyyar, Kakakin ADCn ya ce jagorancin jam’iyyar ya ziyarci ofishin ‘yan sandan jihar, inda aka sanar da shi cewa ‘yan sanda ba su san da zancen ba. Sannan, ya ce rundunar ta yi iƙirarin cewa babu wata hukumar tsaro guda da za ta tilasta rufe ofishin ba tare da sanya ‘yan sanda aciki ba ko kuma samun wani umarni daga kotu. “Sun tabbatar mana da cewa ofoshinmu yana nan a gare mu, don haka babu wani abin tayar da hankali,” inji shi.

By Babaji

Leave a Reply