
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar ADP ta jinjina wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) bisa sake nazari akan lokutan gudanar da babban zaɓen 2027 a ƙarƙashin tsarin dokar ƙasa.
A sanarwar da Shugabanta na Ƙasa ya fitar, ADP ta ce matakin da hukumar zaɓen ta ɗauka akan lamarin ya nuna yadda ta damu da matsayin al’umma akan muhimman al’amuran da take aiwatarwa.
Ta kuma yaba wa INEC bisa nuna a shirya ke ta saurari koken al’umma a yayin da ta yanke hukuncin akan wani al’amari da suka nuna rashin gamsuwa da shi a dokance.
ADP ta ƙara da cewa, yayin da hukumar take ƙoƙarin kiyaye doka da cika sharuɗɗan da ake buƙata akan lamura zaɓe, wajibi ne kuma a yi duba da masalahar al’umma akan harkokin addininsu.
Kazalika, ta ce sanya zaɓe a lokaci azumin watan Ramadana zai yi matuƙar tasiri wajen shiga zaɓe musamman daga ɓangaren al’ummar Musulmi, wanda la’akari da hakan lalurar dimukraɗiyya ce.
Don haka ta shawarci INEC da ta cigaba da kasancewa mai neman shawarwari da masu ruwa da tsaki tare da tabbatar da cewa jaddawalin gudanar da zaɓen da za ta fitar a nan gaba ya yi sanadiyyar shigar jama’a da dama cikinsa.
