
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani a matsayin Jakadan Sabunta Fata (Renewed Hope) kuma mataimakin darakta-janar na wayar da kai, hulɗa da jama’a da kuma tattara magoya baya na jam’iyyar APC gabanin zaɓen 2027.
A wata sanarwa da Kakakin Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar a jiya Talata, ya ce naɗin ya fara aiki ne a nan take.
Ya bayyana cewa an zaɓi Uba Sani ne bisa la’akari da ƙwarewarsa a jagoranci da kuma iya tsara al’amuran siyasa yadda ya kamata a matakai daban-daban.
Ya ƙara da cewa, sabon muƙamin nasa zai haɗa da aiki kafaɗa-da-kafaɗa da darakta-janar na shirin “Renewed Hope Ambassador” tare da shugabannin jam’iyya, musamman shugaban APC na ƙasa.
Ana ganin wannan mataki a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen APC na ƙarfafa tsari da haɗin kai domin tunkarar zaɓen shekarar 2027, inda ake sa ran za a ƙara kaimi wajen wayar da kai da tattara magoya baya a faɗin ƙasa.
