2027: Burina zama shugaban ƙasa ko mataimaki – Kwankwaso ga jam’iyyu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jagoran Jam’iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana aniyarsa cew ba zai haɗe da kowace jam’iyya ba yayin tunkarar zaɓen 2027 matuƙar ba za a ba shi tikitin tsayawa takarar kujerar shugaban ƙasa ko mataimakin shugaban ƙasa ba.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, yayin jawabi ga magoya bayansa a wani taron ‘yan Kwankwasiyya da aka gudanar gidansa da ke Miller Road, Jihar Kano.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake sauye-sauyen sheƙar jam’iyyu acikin ‘yan siyasa don tunkarar babban zaɓen.

Sannan, Injiniya Kwankwaso ya ma magana ne bisa la’akari da makomar jam’iyyar NNPP musamman a Kano bisa rahotonnin da ke cewa akwai yiwuwar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya koka Jam’iyyar APC.

Ya ƙara da cewa, NNPP jam’iyya ce da aka gina bisa amana da sadaukarwa, don haka duk wani yunƙuri na watsi da ita don neman wata jam’iyya zai zama babban kuskure ga duk wanda ya amfana da goyon bayan jama’a a ƙarƙashinta.

A cewarsa, kasancewar APC ke da adadinafi yawa cikin gwamnoni, ba shi ke nuna bada tabbacin nasara a yayin zaɓuka ba, yana mai cewa aiki, riƙo da gaskiya da adalci sune jinshikan samun nasarar zaɓe.

Kazalika, tsohon ministan tsaron ya gargaɗi ‘yan siyasa akan raina hankalin masu zaɓe, yana mai cewa ikon ƙarfin siyasa ya ta’allaƙa ne da jama’a ba tsarin jam’iyya ba kaɗai.

By Babaji