
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rahotanni sun bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya tsoma baki a rikicin da ke tsakanin Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara da Ministan Abuja Nyesom Wike
A cewar wata majiya da ke kusa da Fadar Shugaban Ƙasa, Shugaba Tinubu ya gayyaci Wike domin tattaunawa akan al’amarin, wadda za a gudanar da ita a wajen Nijeriya.
Rahotannin sun nuna cewa Gwamna Fubara ya bar ƙasar a ranar Alhamis ta jirgin haya na musamman, da nufin ganawa da
Shugaba Tinubu a ƙasar Faransa.
Wannan al’amari na zuwa ne a daidai lokacin da wasu ‘yan Majalisar
Dokokin Ribas, waɗanda ake ganin masu biyayya ne ga Wike, suka fara sabon yunƙurin sauke Fubara da Mataimakiyarsa, Ngozi Odu daga kan kujerar mulkin jihar.
An gudanar da haka ne a zaman majalisar da Kakakin Majalisar, Martins Amaewhule, ya jagoranta a ranar Alhamis inda shugaban mafiya rinjaye, Major Jack ya karanta sanarwar zarge-zargen manyan laifuka da ake tuhumar gwamnan da su.
Zarge-zargen guda bakwai sun haɗa da rusa ginin Majalisar Dokoki,
kashe kuɗaɗen gwamnati ba tare da amincewar kasafin kuɗi ba, hana sakin kuɗaɗen da aka ware wa Hukumar Ayyukan majalisa, da kuma ƙin bin hukuncin Kotun Ƙoli kan ’yancin cin gashin kan Majalisar Dokoki.
A ɗaya gefen, an zargi Ngozi Odu, da
almundahana, kashe kuɗaɗen jama’a ba bisa ƙa’ida ba, hana
Majalisar Dokoki gudanar da ayyukanta na kundin tsarin mulki, da kuma ba da dama ga wasu mutane su mamaye ofisoshi ba tare da tantance su ta Majalisar ba.
Kakakin majalisar ya ce, za a miƙa wa Fubara da mataimakiyarsa sanarwar tsige su cikin kwanaki bakwai masu zuwa,
sannan ya ɗage zaman majalisar zuwa ranar 15 ga Janairu.
