
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamiɗo, ya yi watsi da iƙirarin Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima na cewa shi da wasu sanannun ‘yan siyasa a jihar suna goyon bayan jam’iyya mai mulki APC yayin tunkarar zaɓen 2027.
Lamiɗo ya musanta wannan iƙirari ne a wani tsokaci a Facebook da DCL Hausa ta wallafa, wanda a ciki aka wallafa bidiyon da ke nuna Shettima yana cewa fitattun ‘yan siyasa a Jigawa, ciki har da tsohon gwamnan, suna goyon APC.
Da yake magana kan al’amarin, Lamiɗo ya ƙalubalanci dalilin da zai sa ya zama a danganta shi da APC, yana mai tunatar da cewa bai goyi bayan jam’iyyar ba a lokacin da aka kafa ta a 2014 ma ballantana yanzu. “Ikon Allah. Ban yi APC 2014 ba sai yanzu a 2026?” ya rubuta.
Ya bayyana cewa kalaman sun fito ne daga bakin ɗan ƙabilar Kanuri inda ya kammala da karin maganarsu ta “kattuwunum”, wato kalaman ƙarya. Baya ga haka, ɗan siyasar ya kuma wallafa wani saƙon ɗaya daga cikin magoya bayansa da ke musanta kalaman Shettiman.
Ana ganin waɗannan kalamai a matsayin masu kishiyantar tarihin siyasar Lamiɗo, wanda saboda tsayuwarsa ta zama a jam’iyya guda suka sa ya yi fice cikin sauran ‘yan siyasa a Nijeriya, inda ake ganin da Shettima ya san wannan tarihi, da ba zai yi waɗannan zarge-zarge ba.
