2027: Dakta Abraham Ekpo ya tabbatar da niyarsa ta neman takara a hukumance

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Keffi

Ɗan takarar kujerar ɗan majalisar dokokin jihar Nasarawa da ke neman wakiltar mazaɓar Karu-GItata a APC a zaɓen 2027 Dakta Abraham Habu Ekpo ya bayyana niyarsa a hukumance.

Abraham Ekpo ya bayyana haka ne a lokacin da ya jagoranci ɗimbin magoya bayansa inda suka ziyarci ofishin jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Karu.

Daiyake jawabi ɗan takarar ya bayyana cewa zai tabbatar da cigaba masu ma’ana a yankin tare da gudanar da kyawawan ayyukan cigaba.

Yace kawo yanzu duka ‘yan majalisar dokokin da suka wakilci mazaɓar Karu-GItata ɗin duk sun bada nasu gudumawa daidai gwargwado amma shi kam yanaso ne ya fito da sabon tsalon jagorancin yankin ne a majalisar don tabbatar da cigaba mai ɗorewa da zai inganta rayuwar al’ummar a duka matakai inda ya ƙara da cewa tuni ya tsara waɗannan ƙudurorin da kuma yadda zai aiwatar dasu da yardar Allah idan ya yi nasara.

Ya gode wa ɗimbin magoya bayansa da suka fito ƙwansu da kwarkwata suka raka shi zuwa ofishin APC ɗin, musamman manyan baƙi a wajen da suka haɗa da kwamishinan wasanni da matasa na jihar Honorabul Kwanta Yakubu da mataimakin ƙaramar hukumar ta Karu da sauransu tare da fatan Allah ya saka musu da alheri.

Tun farko da suke jawabi daban daban shugabannin jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Karu sun yaba wa kyawawan halayya na ɗan takarar inda suka kuma bayyana cewa tun da ‘yan takara ke ziyartar ofishin ba su taɓa ganin wanda ya tara jama’a kamar shi Dakta Abraham Ekpo ba inda suka ce tabbas hakan na nufin zai yi nasara a zaɓen.

Sun kuma yi amfani da damar inda suka yaba wa ɗan takarar majalisar dokokin Dakta Abraham Ekpo game da gagaruman gudumawa da ya bayar a lokacin da yake riƙe da muƙamin sakataren ƙaramar hukumar Karu din inda suka tabbatar masa cewa za su bashi cikakken goyon baya.

Sauran abubuwa da aka gudanar a yayin taron sun haɗa da miƙawa shugabannin jam’iyyar APC ɗin takardar niyyar fitowa takarar da shi Dakta Abraham Ekpo ya gabatar da ɗaukan hotuna inda su kuma a nasu ɓangaren makada da mawaƙa suka nishaɗantar da jama*a.

By ukarofi