Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina, tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Sautus Sunnah Charity Foundation, sun ƙaddamar da koya wa matasa masu faɗan ƙauranci sana’o’i daban-daban, domin rage ayyukan faɗa da sace-sace da sauran munanan ɗabi’u a cikin al’umma.
An ƙaddamar da wannan shiri ne inda aka tattaro matasa da dama waɗanda suka taɓa shiga harkar faɗan ƙauracin, aka fara horas da su sana’o’in dogaro da kai domin su samu hanyar halal ta rayuwa.
Wannan shiri ba wai koyar da sana’a kaɗai ya ƙunsa ba, har ma da koyar da ilimin addinin Musulunci, tarbiyya da kuma yadda za a zauna lafiya da juna a cikin al’umma. Haka kuma ana ba su shawarwari da nasihohi domin su guji komawa aikata laifuka.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban ƙungiyar Sautus Sunnah Charity Foundation, Sheikh Yakubu Musa Hassan, ya yi kira ga matasan da su ji tsoron Allah a dukkan harkokinsu. Ya bayyana cewa shaye-shaye da rikice-rikice irin na faɗan ƙauraye ba su da wata fa’ida illa jefa mutum cikin halaka.
Ya kuma jaddada muhimmancin riƙe amanar damar da aka ba su, yana mai ƙarfafa musu gwiwa da su mayar da hankali wajen koyon sana’o’in da za su dogara da kansu a nan gaba.
Hakazalika, ya shawarci tubabbun matasan da su kasance masu biyayya ga Allah da Manzonsa, su riƙa gudanar da ibada yadda ya kamata, tare da girmama iyayensu da kuma bin umarninsu, yace hakan ne ginshiƙin samun nasara da ci gaba a rayuwa.
A nasu ɓangaren, wasu daga cikin matasan da suka amfana da shirin sun bayyana jin daɗinsu da godiyarsu ga Gwamnatin Jihar Katsina da kuma ƙungiyar Sautus Sunnah Charity Foundation bisa wannan gagarumin tallafi da suka ce ya sauya musu tunani da rayuwa baki ɗaya.
Sun ce shirin ya taimaka musu wajen gane kurakuransu tare da koyon sana’o’in da za su dogara da kansu. Bugu da ƙari, sun jaddada cewa sun samu tarbiyya da ilimin da ba wai zai amfani su kaɗai ba, har ma zai amfani al’umma gaba ɗaya.
